Rundunar 'yan sandan Nijeriya ta yi kira ga ƙungiyoyin da ke shirin gudanar da zanga-zanga a faɗin ƙasar a watan gobe su miƙa sunaye da adireshinsu ga Kwamishinonin 'yan sandan jihohinsu.
Babban Sufeton 'yan sandan Nijeriya Kayode Egbetokun ne yi kiran a taron manema labarai da ya gabatar ranar Juma'a a Abuja, babban birnin ƙasar.
Kayode Egbetokun ya ce za su ɗauki wannan matakin ne domin kare lafiya da tsaron masu shirin zanga-zangar.
A cewarsa, rundunar 'yan sandan Nijeriya tana sane cewa 'yan ƙasar suna da 'yancin gudanar da zanga-zangar lumana kamar yadda kundin tsarin mulki ya ba su dama, amma bai kamata su wuce-gona-da-iri ba.
“Mun sani cewa kundin tsarin mulkin Nijeriya ya bai wa 'yan ƙasar damar yin zanga-zangar lumana. Amma, domin tabbatar da tsaro da oda, muna kira ga dukkan ƙungiyoyin da ke shirin zanga-zanga su miƙa cikakkun sunayensu da adireshinsu ga Kwamishinonin 'yan sandan jihohin da suke shirin yin zanga-zangar," in ji Kayode Egbetokun.
Ya ƙara da cewa, “domin ganin an yi zanga-zanga cikin nasara ba tare da fuskantar yamutsi ba, muna so masu shirin zanga-zangar su ba mu waɗannan bayanai: wuraren haɗuwarsu da hanyoyin da za su bi a lokacin zanga-zangar da awannin da za su kwashe suna yinta; da sunayensu da cikakken bayani game da shugabannin masu zanga-zangar.”
Batun zanga-zangar, wadda ake shirin gudanarwa ranar 1 ga watan Agusta mai zuwa, ya tayar da hankulan shugabannin ƙasar, inda Shugaba Bola Tinubu ya gana da masu ruwa da tsaki da suka haɗa da gwamnoni da shugabannin addinai da sarakunan gargajiya da sauransu.
Shugaban ya kuma roƙi masu shirin zanga-zangar, wadda aka yi wa taken End Bad Governance a Taurancin Ingilishi, da su janye daga yinta, yana mai shan alwashin biyan buƙatunsu.
Masu shirin zanga-zangar sun ce za su gudanar da ita ne domin tilasta wa gwamnati ta ɗauki matakai daban-daban da suka haɗa da janye matakin da ta ɗauka na cire tallafin man fetur, da magance rashin aikin yi da magace tsadar rayuwa da ƙara albashi fiye da yadda ta yi kwanan baya dai sauransu.