A yayin da ya rage saura kwanaki a rantsar da sabon shugaban Nijeriya, Kotun Sauraron Kararrakin Zabe ta kasar tana ci gaba da bin kadin korafe-korafen da aka shigar na kalubalantar nasarar Bola Ahmed Tinubu na Jam’iyyar APC a matsayin zababben shugaban kasar.
A ranar 25 ga watan Fabrairu aka gudanar da zaben shugaban kasa a Nijeriya, kuma kwanaki hudu bayan nan hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar INEC, ta ayyana tsohon gwamnan jihar Legas a matsayin wanda ya yi nasara bayan ya samu kashi 37 na kuri'un da aka kada.
Sai dai tun a lokacin wasu ‘yan takarar da suka fafata da shi irin su Alhaji Atiku Abubakar na Jam'iyyar PDP da Peter Obi na Jam’iyyar Labour suka shigar da karar kin amincewa da sakamakon.
Dukkansu sun nemi Kotun ta ayyana su a matsayin wadanda suka yi nasara a zaben.
A ranar Litinin 8 ga watan Mayu ne aka soma sauraren kararrakin da 'yan takara na jam'iyyun hamayyar suka shigar.
A wannan makalar, TRT Afrika ta yi nazari Kotun Sauraron Kararrakin Zabe: mece ce ita, kuma mene ne aikinta da huruminta a kan irin wannan lamari?
Mun tattauna da wani babban lauya a kasar Barista Mainasara Kogo, wani lauya da ke Abuja, wanda ya fayyace mana batun.
1. Mece ce Kotun Sauraron Kararrakin Zabe?
Kotun Sauraron Kararrakin Zabe kotu ce da aka yi a matsayin ta wucin-gadi. Sashe na shida na kundin mulkin Nijeriya da sashe na 230 zuwa na 304 sun yi bayani a kan dukkan kotuna na al’ada da ake da su a tsarin Nijeriya.
Kasancewar bai wa hukumar zabe INEC cin gashin kai, shi ya sa aka samar da kotun sauraron kararrakin mai cin gashin kanta don bin diddigin korafe-korafen da suka danganci zabuka a kasar.
2. Mene ne ayyukan Kotun Sauraron Kararrakin Zabe?
Ba a kafa kotun sai bayan an kammala zabe. Tsarin mulkin kasa da dokokin zabe ne suka ba da hurumin cewa za a yi kotun da zarar an yi zabe.
Ita wannan kotun a matakai daban-daban take ba a mazaunin kotu daya ba.
Akwai kotun da ke sauraren kararrakin zabe na gwamnoni da ‘yan majalisun jihohi, sai kuma kotun da ke sauraren kararrakin zabe na ‘yan majalisar tarayya da shugaban kasa, wacce ita ce ta fi karfi.
Kowace kotu a cikin su tana aiki ne daidai da hurumin da aka tanadar mata. Babu kotun da take shiga cikin aikin daya.
Aikinsu shi ne su duba korafe-korafe da suke da su na harkokin yadda aka yi zabe da hanyoyin da ake zargin wasu sun bi sun lalata dokar zabe ko suka saba wa dokar kasa ko tsarin mulkin Nijeriya.
Suna kuma yin duba kan rawar da hukumomin da aka bai wa amana kan harkar zabe suka taka, kamar irin su INEC da jami’an tsaro da jam’iyyun siyasa da wakilan jam’iyyu ko ma ‘yan kasa.
3. Wane irin iko take da shi?
Kotun tana da ikon soke zabe ko cewa a sake yin zabe ko ta ce ga wanda ya ci zabe, ko soke takardar shaidar da aka bai wa wanda ya ci zabe.
A takaice dai tana da karfi sosai a kan duk wasu al’amura da suka shafi cin zabe, kuma tana da hurumin iya yanke hukunci ko na ladabtar da wani ko canza sakamakon zabe, ko bai wa wasu hukumomi umarnin ladabtar da jami'an da aka tabbatar suna da hannu wajen yin wani algus.
Ayyukanta sun dogara ne kan tsaftace harkokin zabe da gyara duk abin da ake ganin ba daidai aka yi ba.
4. Su waye mambobinta?
Ana daukar mambobinta daga alkalai na manyan kotuna.
Ana dauko alkalanta a matakin Babbar Kotun Jiha, a hada a matsayin rundunar sauraron korafe-korafen zaben. A kan daukar daga mutum uku har zuwa biyar.
A lamarin zaben shugaban kasa kuma, babban mai shari'a na Kotun Daukaka Kara shi ne yake hada su da tattara su.
Ita kotun da ta shafi zabukan jihohi ana iya daukaka kararta har zuwa Kotun Daukaka Kara, inda daga nan shari’ar ke tsayawa. Amma a baya kafin sauya dokar, ana iya kai shari’ar har gaban Kotun Koli.
Sai dai shi zaben shugaban kasa har yanzu ana iya daukaka kararsa zuwa Kotun Koli.
5. Yaya wa'adin aikinta yake?
Kotunan Sauraron Kararrakin Zabe na da wa’adi.
Dokar zabe da tsarin mulki sun tanadar wa Kotunan Sauraron Kararrakin Zabe wa’adin kwana 180 daga ranar da aka fara zaman shari’a.
Idan har kotu ta tsaya “biye wa gutsuri tsoma da lauyoyi ke kawowa, to za a dade ba a kammala shari’ar ba,” in ji Barista Kogo.
"Amma idan kotu ta zage ta fuskanci lamarin ba tare da biye wa duk wata gutsuri tsoma ba, to ana iya gamawa da wuri su nade kayansu su bai wa wanda kotun ta gano shi ke da nasara," ya kara da cewa.
6. Mene ne mataki na gaba da ake dauka bayan ta yanke hukunci?
Matakin da ake dauka daya ne cikin biyu.
Ko dai a dauki matakin an amince da hukuncin, wanda ya sha kayen ya mika wuya hukunci ya tabbata a kansa, ko kuma ya ce bai yarda ba a je kotun da ke gaba don daukaka kara.
Ita ma kotu ta gaban na da kwana 180 ta saurari shari'ar ta yanke hukunci.