Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya gabatar da kasafin kudin shekarar 2024 na naira tiriliyan 27.5 (dala biliyan 35) ga majalisun dokokin kasar biyu – majalisar dattawa da ta wakilai.
Shugaban ya bayyana kasafin kudi a matsayin "Budget of Renewed Hope" wato "Kasafin Sabunta Fata" a ranar Laraba.
Tun da farko dai gwamnati ta yi hasashen yin amfani da Naira tiriliyan 26.1 kwatankwacin dalar Amurka biliyan 33.1 a cikin shekarar kudi ta 2024, amma ta sake yin kiyasin zuwa naira tiriliyan 27.5 (dala biliyan 35).
Tinubu ya ba da fifiko kan harkokin tsaro da noma da sufuri, da kiwon lafiya, da dai sauran muhimman sassa, a kasafin kudin, wanda shi ne na farko da ya gabatar a matsayin shugaban kasa.
Kasafin kudin a takaice:
- Jumullar kasafin kudin 2024 - Naira tiriliyan 27.5
- Manyan ayyuka - Naira tiriliyan 8.7
- Ayyukan yau da kullum - Naira tiriliyan 9.92
- Biyan Bashi - Naira tiriliyan 8.25
- Sauyin dala - Kasafin ya ta'allaka ne a kan sauya duk dala daya a kan Naira 750.
Rancen kudi daga waje
A ranar Talata ne Shugaban Kasar ya nemi majalisar dattijai ta bai wa gwamnati damar ciyo bashin dala biliyan 8.6 daga waje don cike giɓin 2022-2024.
Ya ce kudaden da aka karbo za a yi amfani da su ne wajen gina tituna da gyaran su, da samar da ruwan sha da fannin jiragen ƙasa, da haɗa wutar lantarki, da kuma kula da lafiya.
An sha gudanar da jerin zanga-zangar tsadar rayuwa a ƙasar a watanni shidan farko na Tinubu a matsayin shugaban kasa.
Masu zanga-zangar sun zargi shugaban kasar da zama silar tsadar rayuwa bayan cire tallafin fetur da ya yi jim kadan bayan shan rantsuwar kama mulki.
Tinubu ya kuma fuskanci wani babban ƙalubale na karfafa darajar Naira a kan Dalar Amurka, wadda ta kara daraja sosai a kan kudin Nijeriya.