Hukumomi a Laberiya sun binne mutanen ga gobarar tankar gas ta yi sanadin mutuwarsu a ranar Laraba.
An gudanar da jana'izar ne tare da hadin gwiwar kungiyar agaji ta Red Cross ta kasar Laberiya.
Fiye da mutane 40 ne suka mutu a sakamakon hatsarin wata motar dakon gas wacce ta fadi a yankin tsakiyar kasar Laberiya kana gobara ta tashi, kamar yadda babban jami'in kula da lafiya na kasar ya shaida wa kafafen watsa labarai na kasar.
“A kokarin da muka yi, mun samar da jakunkunan saka gawa sannan muka tattara sauran sassan jikin mutanen da suka kone da kuma wadanda suka samu rauni, muna kuma hada gwiwa da hukumomin yankin da kuma hukumar lafiya ta yankin domin tabbatar da an binne mutanen da gobarar ta kashe,” in ji Gregory T. Blamoh, babban sakataren kungiyar agaji ta Red Cross.
Motar tankar da ke dakon mai ta fadi ne a wani rami da ke kan hanyar Totota mai tazarar kilomita 130 daga Monrovia babban birnin kasar ta Laberiya a ranar Laraba.
Dakta Francis Kateh ya shaida wa gidan talabijin na Super Bongese TV cewa zai yi wuya a iya tantance adadin wadanda hatsarin ya rutsa da su domin wasu sun kone kurmus, sai dai ya yi kiyasin cewa mutane sama da 40 ne suka mutu.