Gwamnatin Ghana ta ce tana daukar matakai domin dakile afkuwar wannan lamari. Hoto/Reuters

Akalla mutum 50 suka rasu sa’annan 241 suka samu raunuka sakamakon gobara da aka yi sau 6,796 a kasar Ghana.

Mataimakin Shugaban Ghana Dakta Mahamudu Bawumia ne ya bayyana hakan a lokacin yaye dakarun kashe gobara karo na 23 da aka yi a Ghana inda ya ce gobarar da aka yi a bara kadai ta jawo asarar cedi miliyan 64.

A yayin bikin, mataimakin shugaban kasar ya yi kira ga ma’aikatan kashe gobara na kasar da su rinka samar da shirye-shirye domin wayar da kan jama’a kan kiyaye gobara, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Ghana ya bayyana.

Sai dai mataimakin shugaban kasar ya bayyana cewa za a samu raguwar hakan a hankali sakamakon matakan da gwamnatin kasar ke dauka ciki har da kara kafa wasu makarantun horas da ma’aikatan kashe gobara biyu da kuma makarantun horaswa wadanda ake ginawa a halin yanzu.

Mista Bawumia ya yi alkwarin cewa gwamnatin kasar za ta karo motocin kwana-kwana 200 domin kara taimaka wa bangaren kashe gobara na kasar.

Ya kuma bayyana cewa sakamakon irin abubuwan da ke faruwa, gwamnatin kasar ta bayar da dama a dauki mutum 2,000 aikin kashe gobara domin kara samun sauki.

Jimlar mutum 339 aka yaye a matsayin ma’aikatan kashe gobara wadanda suka hada da maza 210 da mata 129.

TRT Afrika da abokan hulda