Ƴan bindiga da ake zargi mayaƙan ƙungiyoyin da ke iƙirarin jihadi ne sun kashe gomman sojojin Mali ranar Laraba a wani gagarumin hari da suka kai sansaninsu a yammacin ƙasar.
"Fiye da mayaƙa 100 da ke iƙirarin jihad sun kai hari a wani wuri da sojoji suke zama a ƙauyen Kwala," a cewar wani wakilin garin Mourdiah, mai nisan kilomita 300 daga Bamako, babban birnin ƙasar.
"Sojoji da dama sun mutu bayan mayaƙan da ke iƙirarin jihadi sun yi musu dirar mikiya inda kuma suka fice daga yankin ba tare da fuskantar wata matsala ba," in ji wakilin wanda ba ya so a bayyana sunansa.
Wani jam'in gwamnatin ya tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na AFP wannan labari, inda ya ƙara da cewa mayaƙan "sun soma tashin bama-bamai a sansanin sojin" kafin su kashe sojojin.
Kazalika wani ɗan siyasa ya ce an yi ta jin ƙarar musayar harbe-harbe kuma sojojin gwamnati sun koma cikin sansanin bayan sun gama artabu da ƴan bindigar.
Rundunar sojin ƙasar ta fitar da wata sanarwa da ke tabbatar da kai harin, ko da yake ba ta faɗi adadin sojojin da aka kashe ba da kuma muƙamansu sannan ta yi iƙirarin "ganowa da kashe ƴan ta'adda da dama".
AFP ba ta tabbatar da wannan iƙirari ba daga majiyoyi da dama da ta tattaunawa da su a yankin.
Gwamnatin sojin Mali ta kori sojoin Faransa daga ƙasar a 2022 sakamakon taɓarɓarewar rashin tsaro bayan juyin mulkin da aka yi a shekarar 2020 da 2021.
Tuni Mali ta ƙulla ƙawance da Rasha a yunƙurin shawo kan rasin tsaron da ke addabar ta.