Nan ba da dadewa ba Mahamat Idris Deby zai sha rantsuwar kama aiki.

Majalisar tsarin mulkin kasar Chadi ta ayyana shugaban riƙon ƙwarya Mahamat Idriss Deby Itno a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar a ranar 6 ga watan Mayu da kashi 61% na kuri'un da aka kada.

A ranar Alhamis ne majalisar ta yi watsi da kararrakin da ‘yan adawa suka shigar, wadanda suka yi zargin cewa shi ne halastaccen wanda ya lashe zaben, saboda magudin zabe.

Dan takarar jam'iyyar adawa Success Masra, wanda ya zo na biyu da kashi 18.5% na kuri'un da aka kada, ya kalubalanci nasarar Deby bayan da hukumar zaben kasar ta sanar da sakamako a ranar 10 ga watan Mayu.

Kasar Chadi ta kasance kasa ta farko a cikin Ƙasashen Yammacin Afrika da aka yi juyin mulkin da suka koma kan tsarin mulkin kasar ta hanyar akwatin zabe.

Masra ya yi ikirarin shi ya yi nasara

Kafin bayyana sakamakon mako guda da ya gabata, Masra ya yi ikirarin samun nasara a wani jawabi da ya gabatar kai tsaye ta Facebook tare da yin kira ga jami’an tsaro da magoya bayansa da su yi adawa da abin da ya kira yunkurin satar kuri’u.

"Wasu tsirarun mutane sun yi imanin cewa za su iya sa mutane su yarda cewa tsarin da ya shafe shekaru da dama yana mulkin kasar Chadi ya lashe zaben. Ga dukkan 'yan kasar Chadi da suka kada kuri'ar neman sauyi, wadanda suka zabe ni, ina cewa: su haɗa kai su nemi 'yancinsu, amma a yi shi cikin nutsuwa da salama, "in ji shi.

Tabbatar da nasarar Deby yanzu na nufin zai sha rantsuwar kama mulki nan ba da dadewa ba.

Tsaro da tattalin arziki sun kasance muhimman batutuwan yaƙin neman zaɓen.

Daya daga cikin kasashen da ba su da ci gaba a duniya, karancin albarkatun kasar Chadi ya ragu matuka sakamakon manyan matsalolin da suka hada da canjin yanayi da ke haifar da tsananin zafi da rikicin 'yan gudun hijira da ke da nasaba da yakin basasar Sudan.

TRT Afrika