Singh ta ce Amurka ta kammala kwashe dakarunta daga sansanin sojojin sama na Air Base 101 da ke Yamai ranar 7 ga watan Yuli/. Hoto: US Africa Command

Amurka tana ci gaba da tattara komatsenta domin kwashe dukkan dakarunta kusan 1,000 daga jamhuriyar Nijar nan da ranar 15 ga watan Satumba, a cewar Ma'aikatar Tsaro ta Pentagon a ranar Litinin.

"Yanzu haka Amurka tana da kimanin dakaru 300 a Nijar, kuma muna kan hanyar kwashe su cikin aminci ba tare da hargitsi ba nan da 15 ga watan Satumba," a cewar Mataimakiyar Kakakin Pentagon Sabrina Singh a hira da 'yan jarida.

Singh ta ce Amurka ta kammala kwashe dakarunta daga sansanin sojojin sama na Air Base 101 da ke Yamai ranar 7 ga watan Yuli.

A watan Maris Nijar ta kawo ƙarshen dangantakar soji da Washington, inda ta bayyana zaman dakarun Amurka a ƙasar a matsayin "haramtacce" saboda Amurka "tana ƙaƙaba mana sharuɗɗan da ba su dace da dimokuraɗiyya ba kua ba su da gurbi a Nijar," kamar yadda mai magana da yawun gwamnatin sojin ƙasar Amadou Abdramane ya bayyana.

AA