Jamhuriyar Nijar ta fada rikicin siyasa tun bayan da sojoji suka hambarar da Shugaba Mohamed Bazoum a watan Yulin da ya gabata./Hoto:Reuters

Amurka ta yi niyyar ci gaba da kawance da Jamhuriyar Nijar game da harkokin tsaro da ci-gaba muddin sojojin kasar suka dauki matakin dawo da dimokuradiyya, a cewar wata jami’ar diflomasiyyar kasar.

Molly Phee, Mataimakiyar Sakataren Harkokin Wajen Amurka kan Afirka, ta bayyana haka ne ranar Laraba a Yamai bayan ta gana da shugabannin sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar a watan Yuli.

Phee ta ce ta fayyace wa shugabannin sojojin da ake kira CNSP “karara” cewa “muna son sake zama kawaye na gari da Nijar, amma dole ne su ma CNSP su zama nagartattun kawaye ga Amurka.”

“A tattaunawar da muka yi, na tabbatar musu cewa Amurka na shirin dawo da hulda ta tsaro da ci-gaba daki-daki, amma ya kamata su ma CNSP su dauki mataki.”

Amurka ta sanar da hakan ne kwanaki kadan bayan Nijar da Rasha sun sanya hannu kan yarjejeniyar karfafa hulda a fannin tsaro yayin ziyarar da Mataimakin Ministan Tsaron kasar Yunus-bek Yevkurov ya kai Yamai.

Kazalika Amurka ta yi wannan kalami ne bayan da a kwanakin baya sojojin Nijar suka soke yarjejeniyar tsaro guda biyu da Tarayyar Turai.

Masu sharhi sun ce Amurka da sauran kasashen Yamma na cike da fargaba game da kawancen da Rasha ta kulla da Nijar, matakin da ka iya zama barazana a gare su.

Rasha na ci gaba da yaukaka dangantakan tsaro tsakaninta da kasashen Yammacin Afirka, ciki har da Mali da Burkina Faso.

AA