Ambroise N'koh ya ce aikin gona ya fi karɓarsa fiye da aiki a matsayin mai kula da zirga-zirgar jiragen sama./Hoto / TRT Afrika

Daga Firmain Éric Mbadinga

Sauyawa daga manomin Cocoa zuwa mai sarrafa cakuleti yana da wahala kamar yadda yake da matuƙar sha'awa, irin yadda suka haɗu suka samar da kyawawan launi da ɗanɗano.

Ambroise N'koh ya fahimci haka fiye da kowa, tunda ya samu lambobin yabo da yawa sakamakon aikace-aikacensa a gonar Cocoa.

Wannan ɗan asalin Cote d'Ivoire mai shekara 60, mutane da dama sun tabbatar da cewa, shi ne mai sana'ar cakuleti da ya fi kowa a ƙasar ta Afrika ta Yamma kuma yana daga cikin waɗanda suka fi kowa iya sana'ar a duniya.

Ɗaukakar tasa ta zo ne ƙarƙashin aiki tuƙuru na kusan shekara ashirin a fannin aikin gona da gandun daji, tun da ya bar tsohuwar sana'arsa a fannin sufurin jirgin sama a matsayin mai kula da zirga zirgar jiragen sama.

Kimanin kashi 70 na cocoa a duniya yana zuwa ne daga ƙasashen Afrika na Ivory Coast, da Ghana, da Nijeriya da kuma Kamaru, inda Ivory Coast ke kan gaba.

A shekarar 2019, N'Koh mazaunin Abidjan, na ɗaya daga cikin mutane 20 da suka karɓi kyautar Masu Sana'ar Cocoa ta Duniya, wacce shirin samar da Cocoa da ke gano Cocoa da ya fi inganci a duniya, ya shirya.

"Na fara noman Cocoa na gargajiya a shekarar 2006," N'Koh ya shaida wa TRT Afrika. "Shekaru biyu daga bisani, na haɗu da wani da ya ba ni ƙarfin guiwa a sana'ata ta noman Cocoa kuma ɗan kasuwa."

An karrama Anbroise N'Koh a matsayin ɗaya daga cikin masu sana'ar Cakuleti da suka fi iyawa a duniya. Photo / TRT Afrika

Kafin haɗuwarsa da Farfesa Kone Daouda, wanda a wancan lokacin shi ne darakta a Cibiyar Ɗumamar Yanayi Da Bambancin Halittu, fafutukar da N'Koh ya yi a harkar noman cocoa, ta kasance kamar irin ta kowa ne da ya fara harkar da matsaloli suka dabaibaye.

"Na yi magana da Farfesa Daouda a kan matsalolin kiwon lafiya da nake ta fama da su tun da na fara noman cocoa. Ina fama da matsalar numfashi da ta fata. Shawararsa ta sauya komai," N'Koh ya labarta.

Sauyawa zuwa gargajiya

Farfesa Daouda ya shawarci N'Koh da ya yi watsi da yin amfani da kemikal a duk harkokinsa na noman aikin gona da gandun daji, har da noman Cocoa.

"Ya nuna min yadda ake noma a gargajiyance da ya mayar da hankali kan ingancin da manomin da mai amfani da kayan noman za su amfana a ƙarshen lamarin," a cewar mutumin da ke da ƙira mai kyau kuma kullum yana murmushi.

Tunda ya himmatu ya yi nasarar komawa noman gargajiya, N'Koh ya duƙufa ya koyi duk sababbin dabaru da hikimomi a harkar. Ana kan tafiya, ya ƙara da wasu hikimominsa da suka bambanta shi daga sauran abokan harkarsa.

Ambroise N'koh ya gudanar da shiri a kan yadda ake zamar da Cocoa Cakuleti Photo / TRT Afrika

Noman Cocoa na gargajiya ya ƙara ingancin ƴaƴan Cocoa da N'Koh ya kai kasuwa sannan ya yi darajar da ba zai taɓa tunani ba tun da farko.

"Nasarata ta nuna kuskuren waɗanda da farko ba su fahimci zaɓina ba, inda wasu ma suna kiran shawarar da na yanke da cewa kashe kai da kai ne," N'Koh ya ce.

"Ina aiki da Kamfanin Air Afrique lokaci mai tsawo kafin ya dena aiki. Na yanke shawarar na bar su na koma noma saboda wannan ne ya fi dacewa da ni. Na kasance ina matuƙar sha'awarta tun lokacin da na raka kakana ƙauye ina ƙaramin yaro."

Iyali a matsayin Jigo

N'Koh ya ce goyon bayan da iyalinsa suka ba shi ne ya yi sanadiyar samun nasarorin da ya yi kawo yanzu.

"Iyayena sun ba ni ƙwarin guiwar da nake buƙata domin wannan sauyin alƙiblar," ya tuno.

"Wasu daga cikin abokanaina a ɗaya ɓangaren, sun ɗauka na faɗi ƙasa warwas bisa shawarar da na yanke. Idan aka yi la'akari da sana'ata a fannin sufurin jiragen sama, har da tafiye-tafiye zuwa ƙasashen waje, ba su fahimci matakin nawa ba gaba ɗaya."

Matar N'Koh ba ta yanke ƙauna a kan makomarsa a matsayin manomin Cocoa ba, har ma lokacin da yake fafutikar ganin ya miƙe.

"Matata ta gaya mini cewa, 'Je ka zama manomin Cocoa da ya fi kowa a ƙauyenku, kuma na mayar mata da martanin zan zama manomin da ya fi kowa a duniya," ya faɗa wa TRT Afrika.

Manomi abin koyi

Ɗanɗanon Cakulatin da N'Koh ya ke sarrafawa ya zamar da shi abin koyi a fannin noma da samar da abinci. Gonarsa mai girman kadada 50 akai akai tana karɓar baƙuntar masu ziyara da suka zaƙu su san abin da ya sa Cocoa ya zama na musamman, har da ɗaliban sashen aikin gona da ilimin sanin halittu da kuma masu bincike daga Jami'o'i masu ƙawance a Ivory coast da gaba.

Ambroise N'koh a kullum yana da aniyar bayar da bayanai game da abin da ya sani a harkar noman Cocoa. Photo / TRT Afrika

N'Koh ya ɗauki mutane 10 aiki, waɗanda ya koya wa aikin noma ta hanyar da ya zaɓa. Ma'aikatan wucin-gadi na tallafa wa ma'aikatan dindindin ɗin da wajen tsintar Cocoa da kuma sauran ɗawainiya da ake masa.

Bisa matsakaicin ƙiyasi, gonar na samar da tan 20 na Cocoa a kowacce shekara.

Mayar da hankali da N'Koh ya yi a kan noman Cocoa ya cusa masa sha'awa wajen kare muhalli. Mutumin da ƙasa ta bai wa komai, ya ɗaukar wa kansa, ya yi duk iya yinsa, ya zama mai kare halittun Ubangiji.

Da yake nuni da Taron 2023 na Majalisar Dinkin Duniya a kan Sauyin Yanayi na baya bayan nan a Dubai, N'Koh ya yi fatan cewa shawarwarin da aka yanke za a aiwatar da su, domin taƙaita samar da iskar gas mai gurɓata iska, da kuma rage ɗumamar yanayi zuwa ƙasa da ma'aunin digiri selsiyos 2.

"Ina fatan za a samar da manufofin kula da dazuka na cigaba kuma masu kama hankali," ya ce.

TRT Afrika