Ruwa ya shafe kaso mai yawa na birnin tare da raba dubban mutane da muhallansu. Hoto: Bornon Govt

An shafe dare ana ci gaba da aikin ceton jama'ar da ambaliyar ruwa mafi muni cikin shekara 30 ta shafa a birnin Maidugurin Jihar Borno, inda hukumomi da ƙungiyoyi da ɗaiɗaikun mutane suke ta ƙoƙarin kai agaji.

Ambaliyar ta faru ne sakamakon ɓallewar Madatsar Ruwa ta Alau da tsakar daren Litinin, lamarin da ya sa ruwa ya shafe kaso mai yawa na birnin tare da raba dubban mutane da muhallansu.

Shugaban Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Borno, SEMA, Barkindo Mohammed ya bayyana halin da ake ciki a yanzu da cewa "mummuna ne ƙwarai."

A ranar Laraba Barkindo ya ce tun faruwar lamarin hukumarsa ta ƙaddamar da aikin ceto da kuma rarraba buhunhunan yashi.

"A yanzu haka muna kan aikin ceto da kuma rarraba buhunhunan yashi a Gozari. Maganar da nake yanzu haka ni ma na maƙale; mun zo aikin ceton mutane ni da ma'aikatana amma mun maƙale," in ji shi, kamar yadda Jaridar Daily Trust ta rawaito.

Mutane da dama suna cikin yanayin ha'ula'i ba su san inda suka dosa ba saboda babu hanyoyin da za su sada su da yankunan tudun-mun-tsira.

Tun a ranar Talata ƙungiyoyin agaji sun yi ta kiraye-kiraye ga al'umma da su dinga ba da rahotannin dabaru da hanyoyin da suka dace da za a bi don kai wa jama'ar da suka maƙale abinci da sauran kayan buƙatu.

Wasu iyalan kuma da dama sun samu mafaka a kan tituna saboda rashin sanin ina suka dosa sakamakon hanyoyi da suka toshe.

Kamfanin dillancin labaran Nijeriya NAN ya rawaito yadda wani magidanci mai mata biyu da yara shida ya ce bai san inda zai je ba saboda unguwar da danginsa suke babu hanyar da za a bi a je wajen don gadar da take mahaɗa ta rushe.

Za mu magance bala'in ambaliyar ruwa da sabbin tsare-tsarenmu - Gwamnatin Nijeriya

Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu za ta magance kalubalen bala’in ambaliyar ruwa a kasar.

Mataimakin shugaban kasar, wanda ya ba da wannan tabbacin a Maiduguri, babban birnin jihar Borno a ranar Talata, ya bayyana cewa, “duk da cewa abubuwan da ke haifar da bala’in ambaliyar ruwa da sauran bala’o’i da ke faruwa a kasar nan iri-iri ne, amma tuni Shugaba Tinubu ya samar da cikakken tsari da nufin magance matsalar da ma wadannan kalubalen gaba daya."

A ranar Talata ne Mataimakin Shugaban Ƙasar ya isa Maiduguri domin tantance irin ɓarnar da ambaliyar ruwa ta yi wa al’umma a jihar.

Da yake jajanta wa wadanda bala’in ambaliyar ruwa ya rutsa da su, Shettima ya bayyana cewa, ba wai kawai Shugaba Tinubu ya nuna juyayinsa ba ne, har ma ya ba da tabbacin cewa gwamnatin tarayya za ta ba da fifiko ga jin dadin al’ummomin da abin ya shafa.

TRT Afrika