Aljeriya ta juya da 'yan ci-rani kusan 20,000 zuwa Jamhuriyar Nijar waɗanda suka taso daga ƙasashen yankin Sahara zuwa Turai, kuma yawancinsu suna "cikin mummunan hali", a cewar wata ƙungiya mai zaman kanta da ke Yamai mai suna Alarme Phone Sahara a ranar Litinin.
Tun shekarar 2014 'yan ci-rani, waɗanda suka haɗa da mata da yara, suna yawan bi ta Aljeriya a yunƙurin tsallaka Bahar Rum domin isa Turai amma hukumomi a Aljeriya suna juyawa da su.
Ƙungiyar Alarme Phone Sahara -- wadda take ceto 'yan ci-rani daga saharar Aljeriya da Nijar -- ta ce an juya da 'yan ci-rani 19,798 zuwa Nijar daga watan Janairu zuwa Agusta, kamar yadda mai magana da yawunta Moctar Dan Yaye ya bayyana.
Ana yawan barin 'yan ci-ranin cikin "mummunan yanayi" kuma akasari suna faɗawa yanayin "da ke iya kai wa ga mutuwarsu", a cewar ƙungiyar a rahoton da ta fitar a ƙarshen watan Agusta.
"Ana kama 'yan ci-rani idan hukumomi suka kai samae a wuraren da suke fakewa ko inda suke aiki a birane, ko kuma a kan iyaka da Tunisiya sannan a ɗauke su zuwa Tamanrasset (kudancin Aljeriya) kafin a tuƙa su a manyan motocin a-kori-kura zuwa Nijar," in ji Yaye.
Daga nan ne ake ɗaukar 'yan asalin Nijar a motoci zuwa Assamaka, wanda shi ne gari na farko na ƙasar Nijar da ke kan iyaka, inda ake miƙa su ga hukumomi.
Su kuwa 'yan sauran ƙasashe, ana barinsu a wurin da ake kira "ihunka-banza", wani yankin sahara da ke kan iyakar Aljeriya da Nijar.
Daga can, ana tilasta musu su yi tafiyar ƙafa ta kilomita 15 zuwa Assamaka a cikin matsanancin yanayi, a cewar Yaye.
Yaye ya ƙara da cewa da zarar 'yan sandan Nijar da ke Assamaka sun kammala ɗaukar bayanan 'yan ci-ranin za su miƙa su ga cibiyoyin Majalisar Ɗinkin Duniya da Italiya inda ake tsugunar da su, kafin a tafi da su zuwa wasu cibiyoyin da ke arewacin Nijar.
"Muna samun labarai da dama na cin zarafin da jami'an tsaron Aljeriya suke yi wa 'yan ci-rani da ƙwace kayayyakinsu," in ji shi.
Hukumomin sojin Jamhuriyar Nijar sun yi sammacin jakadan Aljeriya a Nijar a watan Afrilu inda suka yi masa ƙorafi kan "mummunan yanayin" da 'yan ci-rani suke fuskanta a ƙasarsa kafin a juya da su zuwa Nijar.
Sai dai hukumomin Aljeriya sun mayar da martani ta hanyar sammacin jakadan Nijar a ƙasarsu, sannan suka bayyana ƙorafin a matsayin "mara tushe".