Shugabancin na shekara ɗaya da Afirka ta Kudu za ta yi kan ƙungiyar ta G20 ta ƙasashe masu ƙarfin tattalin arziƙi zai fara ne daga ranar ɗaya ga watan Disamba ta shekarar 2024. / Hoto: AFP

Afirka ta Kudu ta zama shugabar ƙungiyar G20 ta ƙasashe ashirin masu ƙarfin tattalin arziki inda ta zama ƙasar Afirka ta farko da za ta yi jagoranci ƙungiyar ta ƙasashe masu ƙarfi.

"Na samu darajar karɓar ragamar ƙungiyar G20 ta shekara ɗaya mai zuwa a madadin mutanen Afirka ta Kudu," in ji Shugaba Cyril Ramaphosa a jawabin da ya gabatar yayin da ya karɓi shugabancin ƙungiyar daga Brazil a taron da aka yi a Rio de Janeiro.

Wa’adin shugabancin na shekara ɗaya zai fara aiki ne daga ranar 1 ga watan Disamba.

Ya ce Afirka ta Kudu za ta mayar da hankali kan ci-gaban tattalin arziki ga kowa da kuma da ci-gaba mai ɗorewa, yana mai cewa ƙasar ta ɗauki “haɗin-kai da daidaito da kuma ci-gaba mai ɗorewa” a matsayin taken wa’adin shugabancinta.

Neman muradun MDD masu ɗorewa (SDG)

Ya ce Afirka Kudu za ta nemi ƙarfafa da ƙara neman cim ma muradun Majalisar Ɗinkin Duniya na ci-gaba mai ɗorewa da kuma alƙawarin kauce wa wariya da rashin haƙuri.

"Ko a Gaza ne ko kuma a Sudan ko Ukraine, za mu goyi bayan waɗanda suke fama da wahala," in ji Ramaphosa , yana mai ƙarawa da cewa dole ne ƙungiyar G20 ta tallafa wa ƙasashe da suka fi rauni ta fuskar annoba da kuma matsalolin kiwon lafiya na duniya da ke buƙatar taimakon gaggawa.

Ya ce zai yi aiki wajen daƙile rashin daidaito, wadda wata muhimmiyar barazana ce ga cigaban tattalin arziƙin duniya da kwanciyar hankali, ya kuma sha alwashin gabatar da muradun ci-gaban Afirka da kuma ƙasashe masu tasowa a ajandar ƙungiyar.

An karɓi ƙungiyar tarayyar Afirka a matsayin mamba ta dindin a ƙungiyar G20 a taron ƙungiyar da aka yi birnin New Delhi a shekarar da ta gabata.

TRT Afrika