An samu ƙaruwar cutar Mpox a Afirka a shekarar 2024 da kashi 545% idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata, a cewar Cibiyar Kula da Cututtuka ta Afirka (CDC).
Ya zuwa ranar alhamis 7 ga watan Nuwamba, CDC ta fitar da wani rahoto na samun fiye da mutane 50,000 da ake zargi sun kamu da cutar, kana fiye da mutum 1,000 ne suka mutu sakamakon cutar a ƙasashe 19 na Afirka.
Yankin Afirka ta Tsakiya ya kasance wurin da matsalar ta fi ƙamari, inda aka samu adadi mafi yawa na mutanen da suka da cutar da kuma yawan mace-mace.
Jinkirin da aka samu wajen fitar da kuɗaden da aka yi alƙawari ya kawo cikas ga kokarin dakile yaduwar cutar. Duk da alƙawuran kuɗaɗen da aka yi da ya zarce dala biliyan ɗaya, an samu kaso kadan ne kawai daga ciki.
Rashin cika alkawura
Jean Kaseya, babban darakta CDC na Afirka ya bayyana damuwa kan lamarin a wani taron manema labarai da aka gudanar kai-tsaye a Habasha, yana mai cewa "Alkaluman da muke da su a yau kan kudaden da aka samu bai kai kashi 20 cikin 100 na alkawurran da muka samu ba."
Domin magance matsalar, cibiyar CDC ta Afirka ta ce, ta ware alluran rigakafi 899,000 ga ƙasashe tara da annobar ta fi tsanani.
Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo wadda ta kasance ƙasar da ta fi fama da cutar, za ta sami kaso mafi yawa na alluran rigakafin.
Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ayyana Mpox a matsayin cutar da ke barazana ga lafiyar al'ummar duniya a watan Agustan 2022 saboda sabon nau'inta da ke saurin yaduwa.
Kwayar cutar, wadda za a iya yaɗa ta ta hanyar kusanci ta jiki, kana tana nuna alamomi iri-iri, waɗanda suka haɗa da zazzaɓi, da kuraje, da kumburin wani sassan jiki.