An soma gano cutar ne a 1967 a birnin Margurb na kasar Jamus, inda ta kashe kusan kashi 88 na mazaunansa. An sanya wa cutar sunan Marburg ne saboda a can ta samo asali.
Kwayar cutar Marburg Virus Disease (MVD) da ke da saurin yaduwa, tana sanya zazzabi mai zafi kuma ba a samu rigakafi ko maganinta ba a halin yanzu.
Cutar ta tayar da hankalin masana kiwon lafiyar duniya kuma yanzu haka masana suna ta rige-rigen samun rigakafinta.
Ranar Alhamis, Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, ta tabbatar da cewa karin mutum takwas sun kamu da cutar a Equatorial Guinea, baya ga mutum guda da ya kamu da ita tun bayan barkewarta a watan Fabrairu.
An tabbatar mutanen sun kamu da cutar ne bayan wasu gwaje-gwaje da aka gudanar a kansu a garin Kie Ntem da ke gabashi, da Litoral da ke yammaci da kuma lardin Centro Sur, da ke da iyaka da Kamaru da Gabon,” a cewar wata sanarwa da WHO ta fitar.
Yankunan da aka samu cutar suna da akalla nisan kilomita 150 a tsakaninsu, abin da ke nuna cewa cutar ta watsu sosai.
Daraktan WHO a Afirka Matshidiso Moeti, ya ce samun karin wadanda suka kamu da cutar wata babbar alama ce da ke nuna cewa akwai bukatar a kara kaimi wajen gano masu kamuwa da ita da kuma wadanda suka mutu.
Sabuwar sanarwar da Equatorial Guinea ta fitar na zuwa ne kwanaki kadan bayan Ma’aikatar Lafiya ta Tanzania ta bayyana cewa cutar ta bulla a kasar ranar 20 ga watan Maris a lardin Kagera, inda ta yi sanadin mutuwar mutum biyar, yayin da aka kwantar da mutum uku a asibiti.
Mece ce kwayar cutar Marburg
Marburg, cuta ce da ke saurin yaduwa sannan tana halaka wanda ya kamu da ita cikin gaggawa kamar cutar Ebola. Alamomin cutar sun hada da zabbabi mai zafi da zub da jini.
Kwayar cutar Marburg ta samo sunanta ne daga birnin Marburg na kasar Jamus inda aka soma gano ta a 1967 bayan an shigar da wasu birrai kasar daga Uganda. Daga bisani ma’aikatan lafiya na Jamus da Yugoslavia sun shawo kanta.
Tun daga wancan lokacin, ba a samu barkewar annoba irinta ba a Afirka, sai dai Ebola. Bakewar Marbug mafi girma ta faru ne a Angola a 2005, inda mutane 374 suka kamu sannan 329 suka mutu.
Amma a baya bayan nan wasu kasashe sun bayar da rahotannin barkewar Marburg wadanda suka hada da Ghana da Guinea da Uganda da Kenya da Angola da Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo da Rasha da Zimbabwe da Afirka ta Kudu da Yugoslavia da kuma Jamus.,
Hakan ya sa ake kallonta a matsayin cutar da ta mamaye duniya kamar cutar korona.
Alamomin cutar
Kwayar cutar tana yaduwa tsakanin mutane idan suka yi mu’amala ta kai-tsaye, musamman idan ruwan jiki ko jinni da amai ko bahayar mai cutar suka taba wanda ba shi da cutar. Ana iya daukar cutar daga dabbobi irinsu jemage da birrai.
A cewar WHO, kwayar cutar Marburg tana haddasa zazzabi mai zafi, lamarin da kansa sassan jikin mutum su daina aiki sannan ya mutu.
Yiwuwar mutuwar wanda ya kamu da cutar ya kama daga kasha 24 zuwa 88 cikin dari.
"An tabbatar da kamuwar karin mutum takwas bayan wasu gwaje-gwaje da aka gudanar a kansu a garin Kie Ntem da ke gabashi da Litoral da ke yammaci da kuma lardin Centro Sur da ke da iyaka da Kamaru da Gabon.”
Gano cutar yana da wahala. Marburg da Ebola suna rukuni daya a dangin kwayoyin cutuka, wanda ake kira Filoviridae, kuma suna da alamomin kamuwa da bazuwa iri daya.
Ana iya gane mutumin da ya kamu da kwayar cutar Marburg daga kwana biyu zuwa kwana 21 da shigarta.
Da zarar cutar ta kankama a jikin mutum zai soma yin zazzabi mai zafi. Daga nan sai ciwon kai da amai da ciwon abobin jiki da jijiyoyi da kuma zubar da jini ta ido da hanci da kuma baki.