Tsohon Sarkin Kano Khalifa Muhammadu Sanusi II ya bayyana abin da ya tattauna da sabon Shugaban Nijeriya Bola Tinubu bayan da ya kai masa ziyara a fadarsa da ke Abuja ranar Alhamis.
Basaraken, wanda tsohon Gwamnan Babban Bankin Kasar ne, ya ce yayin ganarwarsu ya gode wa shugaban "dangane da alkiblar da ya dauka kan gyara tattalin arzikin kasar ciki har da cire tallafin fetur da samar da farashin musayar dalar Amurka daya tal da sauransu.
Wadannan abubuwa ne da na dade ina magana a kansu, kuma na yi farin ciki yadda ya fara magance su a ranar farko ta kama aikinsa," kamar yadda ya bayyana wa manema labarai a ganarsa da su a fadar shugaban Nijeriya.
Muhammadu Sanusi II ya gana da shugaban kasar ne kwanaki kadan bayan an cire mutumin da ya gaje shi a shugabancin bankin kasar, Godwin Emefiele, daga kan kujerarsa sannan aka kaddamar da bincike a kan ofishinsa.
Tsohon sarkin ya ce ya kuma tattauna kan rikicin manoma da makiyaya.
"Na ba shi shawarar matakan da suka kamata a fara dauka don magance matsalar. Amma abu mafi muhimmanci shi ne, na yi masa maganar makiyaya 37 da aka kashe a jihar Nasarawa watannin da suka wuce.
Mun rubuta wa tsohon Shugaba Muhammadu Buhari wasika kan batun a lokacin. Yanzu mun rubuta wa [Shugaba Tinubu] wasikar tuni don kada batun ya shiririce. Ya kuma bukace ni da na sake aika masa da wasikar," in ji shi.
Tsohon Sarkin Kanon ya ce batu na uku da suka yi magana a kai shi ne talauci da yadda yara da yawa ba sa zuwa makaranta da kuma karatun 'ya'ya mata a yankin arewacin Nijeriya.
"Za mu ci gaba da tattaunawa da shi don ganin an magance wadannan matsaloli. Idan ba ka samar da ilimi, ciki har da ilmantar da 'ya'ya mata ba, to ba za ka iya kawo karshen matsanancin talauci da matsalar tsaro a arewacin [Nijeriya] ba," in ji shi.
A karshe ya ce ya bai wa sabon shugaban tabbaci cewa a ko da yaushe a shirye yake ya ba da shawara idan bukatar hakan ta taso.