Nijeriya na gudanar da bikin cika shekaru 64 da samun 'yancin kai: Hoto/ TRT Afrika

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya yi jawabi ga 'yan ƙasar a wani ɓangare na bikin ranar 1 ga Oktoba ta samun 'yancin kan ƙasar, inda a yanzu aka cika shekaru 64 da Turawan mulkin-mallaka na Biryaniya suka miƙa wa Nijeriya mulkin kanta.

Ga dai wasu muhimman batutuwa da suka fi jan hankali a jawabin na Shugaba Tinubu:

Gwamnati na yin iya ƙoƙarinta don inganta rayuwar 'yan Nijeriya

Bikin na 1 ga Oktoba na wannan shekarar na zuwa a lokacin da 'yan Nijeriya ke fama da matsalolin tattalin arziki inda rayuwa ta yi tsada kuma suke kokawa ga gwamnati kan ta kawo gyara.

Shugaba Tinubu ya ce sun san halin da jama'a ke ciki, sun ji koken 'yan Nijeriya na tsadar rayuwa da wahalar samun ayyukan yi masu kyau, kuma gwamnati na ayyuka don magance waɗannan ƙalubale.

"A matsayina na shugaban ƙasarku, ina tabbatar muku cewa mun duƙufa wajen neman mafita ta dindindin don kawar da wahalar da 'yan ƙasarmu ke sha," in ji Shugaba Tinubu, yayin da ya sake kira ga 'yan Nijeriya da su yi haƙuri saboda irin sauye-sauyen da gwamnatinsa ke yi sun fara kawo ci gaba.

Kakanninmu sun assasa tushen gina ƙasa jagora a Afirka

A jawabin nasa, shugaban na Nijeriya ya yabi 'yan ƙasa da suka yi gwagwarmayar ƙwatar 'yancin kai tare da zaɓar tsarin dimokuraɗiyya a matsayin salon jagoranci, wadda za ta zama abar koyi ga sauran ƙasashen Afirka.

Ya ce Nijeriyar da aka kafa na da manufar jagorantar sauran ƙasashen Afirka wajen fitar da al'uma daga ƙangin talauci, jahilci da koma-baya, ƙasar da kowanne ɗan Afirka zai dinga alfahari da koyi da ita.

Tinubu ya ci gaba cewa "Bayan shekaru sama da 60, idan muka waiwaya, 'yan Nijeriya a ko'ina suke a ban-ƙasa za su ga yadda muka samu nasara wajen cika burin kakanninmu."

Haɗin kai abin koyi ga sauran ƙasashen duniya

Shugaba Tinubu ya kuma ce duniya na shaida wa tare da amfana da akidar fada-a-cika ta 'yan Nijeriya, inda suke da kwarewa a bangarorin kaifin kwakwalwa, kwarewa a fannin sana'o'i, kimiyya, fasahar kere-kere da gina kasa, wanda su ne irin burin da aka kafa kasar a kai, kuma suna ci gaba da ayyuka don ganin kasar ta ci gaba.

Tinubu ya ce a yayinda ake kokarin mayar da hankali kan yin abubuwan da ba a yi ba da inda aka yi kuskure a matsayin kasa, dole ne mu kalla tare da yaba yadda muka zauna a matsayin kasa daya dunkulallaiya duk da kalubalen da ake fuskanta.

"Tun bayan samun 'yancin kai, Nijeriya ta tsira daga rikice-rikice da hayaniya da dama da suka rusa da karya wasu kasashen duniya da dama. Shekaru shiba bayan samun 'yancin kai, kasar ta fada rikicin siyasa da ya jefa ta yakin basasa. Tun bayan fita daga kangin duhun wancan lokacin, mun koyi rungumar bambance-bambancen da ke tsakaninmu tare da ci gaba da rayuwa mai hadin kai sosai," in ji shugaban na Nijeriya Tinubu.

Ya ce "Duk da kalubale da dama da kasarmu ke fuskanta, amma mun zama masu karfi, hadin kai da kasancewa kasar mai cikakken ikon mulkin kanta."

Kowa ya jajirce don gina Nijeriya

Shugaba Tinubu ya kuma bukaci 'yan Nijeriya da su jajirce tare da sake zage damtse don ganin kasar ta ginu yadda ya kamata.

Ya ci gaba da cewa Nijeriyar da ake bukatar gina wa ita ce wadda za ta amfanin 'yan kasar a yau da kuma gobe, yana mai kira da a yi waiwaye don kar a sake maimaita kura-kuran da aka yi a baya.

"A yayinda muke bikin murnar irin cigaban da muka samu a shekaru 64 da suka gabata, dole ne kuma mu yi duba ga irin damarmakin da muka rasa, da kura-kuran da muka aikatama baya. Idan muna son zama kasa mafi girma a duniya, kamar yadda Ubangiji ya kaddara mana, to dole ne kar mu bar kura-kuranmu su biyo mu a rayuwarmu ta nan gaba," Tinubu ya fada wa 'yan Nijeriya.

"Zabi tsakanin gyara ko ci gaba da durƙushewa"

Wata matsala da ke ci wa 'yan Nijeriya tuwo a kwarya a yau ita ce matsalar tsaro, musamman ma a arewa maso-yammacin ƙasar da ake fama da hare-haren 'yan bindiga da karkuwa da mutane don neman fansa, sai arewa maso-gaba da ke fama da rikicin 'yan ta'adda da ke iƙirarin jihadi.

A yankin kudu maso-gabashin Nijeriya ana fama da rikicin 'yan a-ware, yayin da yankin kudu-maso kudu kuma ke fama da rikicin ɓarayin mai da fasa bututu wanda ke shafar yawan albarkatun mai da Nijeriya ke fitarwa. Yankunan kudu maso-yamma da arewa ta tsakiyar Nijeriya kuma na fuskantar rikicin manoma da makiyaya.

Da yake bayanin yadda gwamnatinsa ke ƙoƙarin shawo kan wannan matsalar, shugaba Tinubu ya ce ya karɓi gwamnati watanni 16 da suka gabata a wata gaɓa mai matuƙar wahala.

Ya ce "Tattalin arziki ya shiga halin ni-'ya-su, al'amuran tsaronmu sun gama taɓarɓarewa. Mun tsinci kawunanmu a hanya mai wahala, wadda zaɓin da ya rage mana shi ne ko dai mu kawo gyara ko mu ci gaba da bin hanyar durƙushewa. Mun zaɓi gyara tattalin arziki, siyasa da fasalin tsaronmu."

Shugaba Tinibu ya shaida wa 'yan Nijeriya cewa gwamnatinsa na samun nasarar yaƙi da ta'addanci da hare-haren 'yan bindiga.

Ya ce "Manufarmu ita ce mu kawar da dukkan barazanar 'yan Boko Haram, masu garkuwa da mutane don neman fansa, 'yan bindiga da duk wani nau'i na tsaurin ra'ayi. A cikin shekara guda, gwamnatinmu ta kassara kwamandojin 'yan ta'addar Boko Haram da masu garkuwa sama da kowanne lokaci a ƙasar."

Tinubu ya ƙara da cewar tun bayan hawansa mulki sojojin ƙasar sun kashe kwamandojojin Boko Haram da 'yan bindiga sama da 300 a yankunan arewa maso-gabas da arewa maso-yammacin ƙasar.

A ranar 1 ga Oktoban kowacce shekara Nijeriya ke bikin murnar samun 'yancin kai daga Turawan mulkin-mallaka na Birtaniya, inda a bana take cika shekaru 64 da samun 'yancin kai.

TRT Afrika