Daga
Abdulwasiu Hassan
Bandaki yana daya daga cikin abubuwa mafiya muhimmanci a rayuwarmu. Wannan dalili ya sa gina bandakunan kasuwa ya zama wata babbar sana'a mai kawo riba a Afirka da sauran sassan duniya.
Nijeriya tana bukatar akalla bandakuna miliyan 11 daga nan zuwa shekarar 2025, ko kuma bandakuna miliyan 3.9 a kowace shekara idan tana so ta kawo karshen matsalar bahaya a fili, daya daga cikin muradu masu dorewa na Majalisar Dinkin Duniya.
"Gina dakunan bahaya da 'yan kasuwa suke yi shi ne mafita dangane da warware matsalar tsaftar muhalli ta gaggawa," in ji Dokta Jane Bevan shugaban da ke kula da Asusun Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) bangare ruwa da tsaftar muhalli (WASH), yayin da ake wani babban taro kan masu harkar gina bandakuna don riba a Abuja kwanakin baya.
Adamu Umar, wani wanda yake harkar gina bandakuna ne don riba a wajen Abuja, yana daya daga cikin 'yan kasuwa da ke kokarin taimakawa wajen shawo kan matsalar bahaya a fili a Nijeriya.
Umar ya fara harkar gina bandakuna ne shekara 20 da suka wuce bayan ya ga wani dan uwansa ya samu nasara a harkar.
Abuja gari ne da yake da wasu unguwanni marasa tsari wadanda dubban ma'aikata ke zaune da kuma wasu masu neman ci gaba a rayuwa.
Yayin da Umar ya fara harkar ya fara samun riba, kodayake daga bisani ya ci karo da kalubale.
Gidan da bandakunansa suke yana cikin gidajen da Hukumar da ke Kula da Babban birnin Tarayyar Abuja (FCTA) ta rusa saboda an gina sa ba tare da karbar izini ba bayan shekara ta 2000.
Damarmaki
Gina bandakuna dama ce ta kasuwanci da ke jiran a bunkasa ta ba wai kawai a Nijeriya ba. Kasashe da dama da ke yankin kudu da hamadar Sahara suna fuskantar matsalar karancin bandakuna, wanda hakan yake kawo barazana ga burinsu na kawo karshen matsalar yin bahaya a fili nan da shekarar 2025.
"Yin bahaya a fili yana gurbata ruwan sha kuma yana kawo yaduwar cututtuka kamar Kwalara da gudawa da kuma atini.
Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta yi hasashen cewa rashin tsaftace muhalli yadda ya dace yana jawo mutuwar mutane 432,000 sanadin gudawa a kowace shekara," a cewar Bankin Duniya.
Akwai akalla mutum 779 a Afirka da ba su da bandakuna masu tsafta, kamar yadda Daraktar Hukumar WHO na Afirka Dokta Matshidiso Moeti ya bayyana a ranar Bandaki ta Duniya a bara.
Bayanai daga UNICEF sun nuna cewa kaso 71 cikin 100 a Jamhuriyar Nijar suna yin bahaya ne a fili. Gaba daya, mutum miliyan 122 da ke rayuwa a yammaci da tsakiyar Afirka ba su da zabi da ya wuce yn bahaya a fili.
A kasar Togo, mutum miliyan uku cikin miliyan tara na 'yan kasar ba su da bandaki, kamar yadda UNICEF ta bayyana. Haka zalika, daya cikin 10 na 'yan Jamhuriyar Dimokradiyyar Kongo suna yin bahaya ne a fili.
Alherai da matsaloli
“Ina samun naira 100,000 zuwa 120,000 (dala 131 zuwa dala 157) a kowane wata da bandakunan da na gina," in ji John Nankat, wani da ya gina bandakuna tsawon shekara 10 a Nijeriya, kamar yadda ya shaida wa TRT Afrika.
Bandakunansa 10 a Mararraba Aso a jihar Nasarawa wadda ke gabas da Abuja, suna fuskantar kalubale mafiya yawa da suka jibanci wayar da kan mutane kan muhimmancin tsafta.
"Da yawa daga cikin masu shiga bandakunan suna bata su ta hanyar barin bahaya a bakin matsugunin, su a tunaninsu saboda sun biya kudi, to sai a yi amfani da su wajen gyara kazantar da suka bari," in ji shi.
"Haka kuma muna kashe makudan kudi wajen kula da bandakunan, muna amfani da sinadarai wajen wanke su saboda kada kwastomominmu su dauki cuta faga junansu."
Kwashe bahayar daga lokaci zuwa lokaci yana daya daga cikin kalubalen da John yake fuskanta wajen tafiyar da bandakunansa.
Bayan shekara 20 na gudanar da bandakunan da ya gina a Abuja, Umar ya amince cewa "kwashe bahayar yana daga cikin manyan kalubale."
Daya daga cikin bandakunan da Umar ya gina a Madalla, a kusa da Abuja, ba ya kawo masa kudi kamar yadda sauran suke yi wadanda suke Abuja. Saboda rashin kayan more rayuwa idan aka kwatanta da tsakiyar birnin Abuja, wannan ya sa dole ya kashe kudi a sabbin wuraren.
Rawar da masu zuba jari za su taka
John ya yi amannar cewa akwai bukatar a kara wayar da kan jama'a kan illolin da ke tattare da yin bahaya a fili da zubar da shara ba bisa ka'ida ba. Idan aka fahimci haka, mutane da yawa za su rika rububin zuwa bandakunan kasuwa maimakon yadda ake samu a baya.
Masu bandakunan kasuwa a daya bangaren ya kamata su mayar da hankali kan tsafta ta hanyar amfani da sinadaran wanke bandakuna da kashe kwayoyin cuta.
"Gwamnati za ta taimaka ta wannan fuskar wajen samar tsarin kwata da tattara shara a birane, da kuma samar da hanyoyin kwashe shara da manyan motoci a farashi mai rashusa," in ji Umar.
A yi wani tsari na ware fili don gina bandakunan al'umma wani abu ne da shi ma ake da fatan yi. Umar a cewarsa ya ce ya kamata duk wani da yake son shiga harkar ya amfana maimakon kawai a ce manyan masu zuba jari ne suka amfana da na kusa da shugabanni.
Kamar yadda ya ce, ya kamata gwamnati ta bullo da wani shirin bayar da rance ga jama'a wadanda suke son shiga harkar saboda a kara yawan bandakunan kasuwa a cikin kankanin lokaci.
Wasu suna ganin ya kamata kasashen Afirka su rubanya kokarinsu wajen samar da bandakuna na gwamnati karin a kan 'yan kasuwa da ake da su.