Emmerson Mnangagwa ya yi fice a siyasar Zimbabwe.
Dan siyasar, mai shekara 80, ya dade yana bayar da gudunmawa a duk wata shawara da ake yankewa ta siyasa a Zimbabwe – tun kafin kasar ta samu ‘yancin kai.
An haife shi a ranar 14 ga watan Satumbar 1942, a birnin Zvishavane wanda ake hakar ma’adinai da ke kudu maso tsakiyar Zimbabwe.
Iyayensa, Mafidhi da Mhurai Mnangagwa, manoma ne sai dai lokaci zuwa lokaci sun rinka siyasa tun a zamanin Turawan mulkin-mallaka.
Mahaifin Mnangagwa ya zama shugaban kauyensu, kuma Turawan mulkin-mallaka ne suka masa sarautar a shekarun 1940.
Shugaban kasar na da ‘yan uwa na jini da suke uwa daya uba daya guda tara sa’annan yana da wasu ‘yan uba saboda mahaifinsa ya auri mata ta biyu.
Yadda Mnangagwa ya hadu da Mugabe
Mnangagwa dan kabilar Karanga ne, kabila mafi girma daga cikin manyan kabilun Shona na Zimbabwe.
Daga baya an bukaci mahaifinsa ya koma Mumbwa da ke tsakiyar Zambia bayan an samu sabani da Turawan mulkin-mallaka. A nan ne Mnangagwa ya hadu da Robert Mugabe wanda daga baya ya zama shugaban kasa.
A lokacin, Mugabe yana aiki a a kwalejin horar da malamai ta Lusaka babban birnin Zambia inda ya rinka zama da iyalan Mnangagwa.
Mugabe, wanda ya kasance mai baki da kuma tsattsauran ra’ayi, ya ja hankalin Mnangagwa domin shiga kungiyar yaki da Turawan Birtaniya a farkon shekarun 1960.
Masu yaki da mulkin-mallaka da dama na Zimbabwe ciki har da Mugabe da Mnangagwa sun yi hadin-gwiwa a 1962 inda suka kafa kungiyar Zimbabwe African People’s Union (ZAPU).
Jim kadan bayan an samar da ZAPU, Mnangagwa na daga cikin matasan jam’iyyar da suka tafi China da Masar domin samun horon aikin soji.
A 1964, sai ya koma Zimbabwe. Wasu daga cikin wadanda suka kirkiro ZAPU wadanda suka hada da Mugabe, sai suka bar kungiyar inda suka kafa Zimbabwe African National Union (ZANU.) Sai Mnangagwa ya bi Mugabe zuwa ZANU.
Kungiyar Crocodile
A 1965, Mnangagwa ya jagoranci kungiyar wasu mayaka wadda ake kira Crocodile Gang domin gudanar da zanga-zanga kan wariyar launin fata.
A wannan lokacin ne ya samu lakabin “crocodile” ko kuma “ngwena” da harshen kasar. An zargi Mnangagwa da tayar da bam a wani jirgin kasa a Masvingo a lokacin neman ‘yancin kan Zimbabwe.
Daga baya an yanke masa hukuncin kisa a 1965, sai dai lauyoyinsa sun kafe kan cewa bai kai shekara 21 ba, wanda hakan ke nufin ba za a iya rataye shi a lokacin ba.
Daga nan ne aka masa daurin zaman shekara goma a gidan yari. Sai ya sake haduwa da Mugabe a gidan yari.
Bayan ya kammala zamansa na gidan yari, sai aka sake shi a 1975 inda aka tasa keyarsa zuwa Zambia mai makwaftaka, inda ya karanci shari’a.
A lokacin da yake Zambia, sai ya ci gaba da zumunci akai-akai da Mugabe. A 1977, sai Mugabe ya bayyana Mnangagwa a matsayin mai taimaka masa na musamman.
Sai Mnangagwa ya zama shugaban farar hula da sojoji na kungiyar Zimbabwe African National Union – Patriotic Front (ZANU-PF).
Ministan tsaro na farko
A ranar 18 ga watan Afrilun 1980, Zimbabwe ta samu ‘yancin kai daga Turawan Birtaniya inda aka sanar da Mugabe a matsayin Firaiministan kasar. A lokacin ne aka nada Mnangagwa a matsayin ministan tsaron kasar na farko.
A ranar 18 ga watan Afrilun 1987, sai Mugabe ya sauya kundin tsarin mulkin kasar inda ya zama Shugaban Zimbabwe na farko.
Tsakanin 1988 zuwa 2000, Mnangagwa ya zama ministan shari’a da na harkokin majalisa inda kuma na dan wani lokaci ya rike mukamin ministan kudi bayan da Ariston Chambati wanda shi ne ministan kudi na lokacin ya rasu.
A shekarar 2000, Mnangagwa ya yi rashin nasara a zaben ‘yan majalisa. Ganin cewa ba ya so abokinsa wanda ya dade da shi ya bar siyasa haka, sai ya zabi Mnangagwa domin zuwa majalisa.
Sai Mnangagwa ya je ya yi takarar shugaban majalisar wakilai inda ya shafe shekara biyar kan kujerar, tsakanin 2000 zuwa 2005. A 2005, sai aka nada shi ministan gidajen karkara da jin dadin jama’a, mukamin da ya rike har zuwa 2009.
Zaben 2008
Zaben 29 ga watan Maris din 2008 ya kasance wani irin zabe na daban ga Mugabe. Babban abokin takararsa Morgan Tsvangirai ya fi yawan kuri’u a zagayen farko, amma an je zagaye na biyu a zaben.
Masu sa ido kan zabe sun bayyana cewa Mnangagwa ne ya yi ruwa ya yi tsaki domin ganin cewa Mugabe ya yi nasara domin ci gaba da zama shugaban kasa.
An raunata daruruwan ‘yan adawa da kuma kashe su, a abin da aka rinka kallo a matsayin wani mummunan yunkuri na hana ‘yan adawa a kasar. Tsakanin 2009 zuwa 2013, Mnangagwa ya kasance ministan tsaro na Zimbabwe.
A ranar 31 ga watan Yuli, Mugabe ya sake karawa da Tsvangirai a zaben shugaban kasar.
Duk da haka Mugabe ya ci zaben mai cike da takaddama da kuri’u miliyan 2.1 fiye da Tsvangirai mai miliyan 1.2. Bayan ya zama shugaban kasa a karo na bakwai, sai Mugabe ya nada Mnangagwa a matsayin mataimakin shugaban kasa
Hannun riga
Mnangagwa ya ci gaba da rike wannan mukamin har zuwa farkon Nuwambar 2017, a lokacin da Mugabe ya kore shi kan zargin “rashin biyayya”.
Haka kuma shugaban ya kuma zargi Mnangagwa da kokarin kifar da gwamnatinsa ta kowace irin hanya, daga ciki har da amfani da maita, zarge-zargen da Mnangagwa ya musanta.
“Shi (Mnangagwa) ya je coci wurin malamai domin ya gano yaushe Mugabe zai rasu. Sai dai an shaida masa cewa shi zai soma mutuwa,” kamar yadda Mugabe ya shaida wa magoya bayansa a Harare babban birnin kasar a ranar 8 ga watan Nuwambar 2017.
“Ya dauka ta hanyar kusanta ta, zan goya shi a bayana har zuwa kujerar shugaban kasa. Sai dai ban mutu ba, ban kuma sauka daga mulki ba,” kamar yadda Mugabe ya kara da cewa.
“Muna fata za mu yi maganin sauran wadanda suka yi makirci tare da shi.” A hankali sai aka rinka yada cewa Mugabe na son ya mika mulki zuwa ga matarsa, Grace Mugabe.
Sai Mnangagwa ya gudu zuwa Afirka ta Kudu a ranar 6 ga watan Nuwamba, inda ya yi ikirarin cewa rayuwarsa na cikin hatsari.
“Tafiyata cikin gaggawa ta faru ne sakamakon ci gaba da barazana kaina da rayuwata da iyalina daga wadanda a baya suka yi ta kokari ta hanyoyi daban-daban domin su kawar da ni har da guba,” in ji Mnangagwa.
Karshen Mugabe
Bayan wasu ‘yan makonni, an tilasta wa Mugabe barin ofis inda Mnangagwa ya maye gurbinsa.
Zimbabwe ta yi zabenta na farko babu Mugabe a ranar 30 ga watan Yulin 2018 a lokacin da aka sanar da Mnangagwa a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa inda ya doke Nelson Chamisa.
Ya samu kuri’u miliyan 2.46 (kashi 51) inda ya yi nasara a zaayen farko kan Chamisa mai kuri’u miliyan 2.15 (kashi 45.07).
An sake yin wani zaben tsakanin mutanen biyu a ranar 23 ga watan Agustan 2023 inda Mnangagwa ya sake yin nasara.
A ranar Asabar da dare, hukumar zaben Zimbabwe ta sanar da cewa Mnangagwa mai shekara 80 na Jam’iyyar Zimbabwe African National Union – Patriotic Front (ZANU-PF) ya samu kuri’u miliyan 2.35 (kashi 52.6) domin samun nasara a zagayen farko.
Wanda ke binsa a baya kamar a zaben baya shi ne Nelson Chamisa na Jam’iyyar Citizens Coalition for Change (CCC) da kuri’u miliyan 1.97 (kashi 44).
‘Makoma mai haske ga ‘yan Zimbabwe
Mnangagwa ya yi alkawarin samar da “makoma mai kyau ga ‘yan Zimbabwe” idan aka sake zabensa.
Sai dai ‘yan adawa sun bayyana cewa rashin gaskiya ya dabaibaye zaben. Mnangagwa ya kara da cewa a wani jawabi a ranar Lahadi zai mayar da hankali kan wadatar da abinci da hada kan kasa da kuma kara wanzar da zaman lafiya a cikin shekaru biyar da zai kara yi.
Zababben shugaban kasar na da ‘ya’ya shida da matarsa da ta rasu, Jayne Matarise.