Kasar Kenya da ke Gabashin Afirka na daya daga kasashen nahiyar da ke jan hankalin 'yan yawon bude ido. / Hoto:AFP

Daga Brian Okoth

A ranar Talata, Kenya ta zama kasa ta farko a duniya da ta cire sharadin biza ga matafiya 'yan kasashen waje.

A jawabin da shugaban Kenya William Ruto ya yi, ya bayyana wannan ci-gaba a matsayin 'na tarihi', inda ya kara da cewa akwai binciken kimiyya da ya tabbatar da cewa kasar da ke Gabashin Afirka ce asalin dan adam ya fara rayuwa a doron kasa.

Wannan sanarwa ta zo a Ranar Cika Shekaru 60 da Samun 'Yancin Kenya.

"Daga watan Janairu, 2024, Kenya za ta zama kasar da ba a bukatar biza don ziyartar ta.

"Daga wannan lokaci ba dole ba ne sai ka nemi biza idan za ka je Kenya dga kowacce kasa ta duniya," in ji Shugaba Ruto, a yayin jawabi a Lambun Uhuru da ke kudu maso-yammacin birnin Nairobi.

Cike bayanai ta yanar gizo

A madadin biza, gwamnati ta kaddamar da tsarin "cike bayanai ta yanar gizo" da zai "tabbatar da an san duk wani wanda zai zo Kenya kafin su karaso zuwa kasar."

"Dukkan matafiya za su nemi izini ta intanet kafin su taho Kenya," in ji Ruto, yana mai cewar akwai sharadin gudanar a bincike kafin tasowa zuwa kasar.

Ministan Harkokin Wajen Kenya Musalia Mudavadi a wata sanarwa ya bayyana cewa yana goyon bayan matakin da shugaban kasar ya dauka na janye sharadin visa ga kowa da kowa.

Babban Sakataren Harkokin Kasashen Waje Korir Singoel ya shaida wa TRT Afirka cewa Kenya na da hakkin karbar mutum ko akasin haka, ma'ana "ba kowa za a bari ya shiga kasar ba."

'Cike bayanka ka jira'

"Dole ne mutanen da ke son zuwa Kenya su shigar da bayanansu a shafin intanet da aka tanada wand anan da dan wani lokaci za a bayyana shi ga jama'a," in ji Sing'oel.

"Da zarar mutum ya shigar da bayanansa shafin intanet, Kenya tare da hadin gwiwa da kasar da mutum ya fito, za su gudanar da binciken tsaro game da mutum, kafin a dauki matakin ba shi damar zuwa kasar ko kuma hana shi," in ji Babban Sakataren, kuma daga baya za a sanar da mutum sakamakon binciken.

Sing'oel ya kuma ce mutane za su jira na tsawon mako guda ko makonni biyu, don su san matsayinsu, kuma babu wani kudi da mutum zai biya.

Babban Sakataren ya kara da cewa nan kusa za a fitar da "bayanai sosai" game da abubuwan da shafin yanr gizon zai kunsa wanda matafiyi zai gabatar kafin ya samu izinin tafiya Kenya, bayan gwamnatin ta gudanar da wani taron ma'aikatun kasar.

Tsawon lokacin tunani kan matakin

An dauki lokaci mai tsawo ana ta tunani kan wannan mataki da Kenya ta dauka na jan hankalin 'yan kasashen waje zuwa kasar.

Shugaba William Ruto a ranar 12 ga Disamba 2023 ya ce za a baiwa 'yan kasashen waje damar shiga kasar ba tare da visa ba daga 1 ga Janairu 2024. / Hoto: Reuters

A watan Afrilun 2009, kwamnatin lokacin karkashin Shugaba Mwai Kibaki ta rage kudin visa da kashi hamsin ga manya, sannan 'yan kasa da shekaru 16 kuma gaba daya.

Gwamnatin ta ce wannan mataki zai karfafa gwiwar masu yawon bude ido zuwa kasar.

A watan Yulin 2011, Ministan Kudi na wannan lokacin Uhuru Kenyatta ya ske dawo da biyan kudin visa, yana mai cewa sashen kula da shige da fice na bukatar kudaden gudanarwa da yawa. Tun wannan lokain ba a canja farashin ba.

An dakatar da kudin visa

Gwamnati ta bayyana cewa ana biyan dalar Amurka $50 don karbar visar zuwa Kenya sau daya, da kuma dala $100 don samun wadda za a iya shuga da ita kasar sama da sau daya.

A farkon watan Nuwamban 2023, Kenya ta sanar da shirin ninka kudin visa, amma sai aka dakatar da shirin.

Matakin janye sharadin visa da kudin neman izinin shiga Kenya zai janyo wa gwamnatin Ruto gibin kudaden da take samu, duba da yadda a baya-bayan nan gwamnati ta karbi Shilling din Kenya biliyan 10, daidai da dala miliyan $65 daga hukumar kula da shige da fice kadai.

Ga shugaban kasa da yake ta kokarin kara yawan kudaden shigar Kenya tun bayan shigar sa ofis a watan Satumban 2022, Ruto na fatan cire visa din zai kara yawan masu yawon bude ido zuwa kasar.

Daduwar alkaluman masu yawon bude ido

Kasar ta Gabashin Afirka ba ta sake kafa tarihin masu yawon bude ido kamar na 2019 ba, a lokacin da ta samu dala biliyan $1.93.

A 2022, kasar wadda ke da lamubunan dambobin dawa, wuraren tarihi, al'adun gargajiya masu kayatarwa da gabar teku mai tsayi, ta samu dala biliyan 1.75 daga harkokin yawon bude ido.

A kalla 'yan yawon bude ido miliyan 1.5 ne suka ziyarci kasar a shekarar.

A yayin da Kenya ke fatan samun karin masu yawon bude ido, da kuma damarmakin kasuwanci idan sun samu, akwai damuwa game da cire sharadin visa domin ziyartar kasar.

Wasu masu nuna tantama cewa tsananta bincikar matafiya, ciki har da duba ko suna da tarihin aikata wani mugun laifi, wanda ake yi yayin neman biza, na tabbatar da an bai wa 'yan kasar waje nagari izinin shiga Kenya.

'Makamin nuna kauna ga kai da alfahari'

"Matakin gwamnati game da visa na da tasiri kan sha'anin tsaro. Biza, a kowacce kasa ta duniya ba wai tana da manufar kara yawan maziyarta ba ne, ana kuma amfani da ita wajen tantancewa da tabbatar da tsaron kasa," in ji Macharia Munene, farfesa a sashen nazarin Alakar Kasa da Kasa a Jami'ar Kasa da ta Kasa ta Amuka, yayin tattaunawarta da TRT Afirka a Nairobi.

Ya kara da cewa "Har a lokacin d aake aiki da sharadin visa, maziyarta d ake son zuwa Kenya na yin wannan abu, d akudi ko babu kudi, ko kuma shan wata wahala."

Gitile Naituli, farfesa kan shugabanci a Jami'ar Meltumedia d ake Kenya, ya bayyana cewa "diflomasiyya cude ni in cude ka ce".

Naituli ya ce "Kana janye visa ga 'yan kasashen da su ma suka janye wa 'yan kasarka/ A matsayin gwamnati, bai kamata ka kyale kowa ya shiga kasarka ba.

Biza wata makami ce na nuna kaunar kai da alfahari. Iyakoki za su zama a bude ga mutane ne kawai bayan an yi duba da nazari na tsanaki."

Ma'ajiyar bayanan aikata muggan laifuka

Ministan Bunkasa Harkokin yawon Bude Ido na Kenya Alfred Mutua ya shaidawa TRT Afirka cewa gwamnati za ta dogara ne kan ma'ajiyar bayananan muggan laifuka ta bai daya don gano bata gari daga cikin matafiya da ke niyyar shiga Kenya.

"Kaso 9.99 na dukkan matafiya 'yan kasashen waje nagari ne. Kaso 0.1 ne kawai batagari. Sai mun duba ma'ajiyar bayanan aikata muggan laifuka ta bai daya kafin mu baiwa mutum damar shiga Kenya."

Wata damuwa ta daban kuma ita ce: kasashe nawa ne za su bayar da irin wannan dama ga ga Kenya?

A Afirka, akwai kasashe 20 da suka baiwa 'yan Kenya damar shiga ba tare da visa ba, wasu 15 kuma suke da tsarin biza a kan iyaka.

A duk duniya, akwai kasashen duniya 76 da 'yan kasar Kenya za su iya shiga ba tare da visa ba.

TRT Afrika