Babban Hafsan Tsaron Nijeriya Janar Christopher Musa ya ce ya ziyarci takwaransa na Jamhuriyar Nijar Birgediya Janar Moussa Salaou Barmo ne domin ƙarfafa dangantakar tsaro da ke tsakanin maƙotan biyu.
Janar Musa ya shaida wa manema labarai ranar Laraba jim kaɗan bayan kammala ziyarar tasa cewa maƙasudin zuwansa Nijar shi ne neman maido da haɗin-gwiwa a tsakaninsu domin ci gaba da tunkarar rashin tsaron da ya addabi ƙasashen biyu.
"Mu sojoji ba 'yan siyasa ba ne. Maganganun da muka yi yau sun shafi yadda za mu haɗa kai mu ƙara tsaron ƙasashenmu guda biyu. Mun san cewa Nijeriya da Nijar 'yan'uwa ne. Tun ba yau ba muna aiki tare, muna atisaye tare. Shi ya sa muka ga ya kamata tun da an ɗan daɗe ba mu yi aiki tare ba, to yanzu yana da kyau mu ci gaba da aiki tare," in ji Janar Christopher Musa.
Ya ƙara da cewa dakarun ƙasashen biyu sun yi nazari kan abubuwan da suka faru tun bayan juyin mulki da sojoji suka yi a Nijar a 2023, inda suka ga "ya kamata mu ci gaba da hulɗa yadda muke yi a da."
Babban Hafsan Tsaron Nijeriya ya yi zargin cewa wasu mutane suna amfani da saɓanin da aka samu tsakanin Nijeriya da Nijar domin ci gaba da haddasa rashin jituwa tsakanin ƙasashen biyu.
Ya ce, "Kafin wannan matsalar ta shigo tsakani aka ɗauki mutane suna so su kawo saɓani a tsakaninmu. Mun ga cewa rashin magana yana sawa abin yana yaɗuwa shi ya sa muka ga ya kamata mu zo mu zauna domin mu fahimci juna. Akwai mutanen da suke son kawo tashin hankali a tsakaninmu."
A nasa ɓangaren, Babban Hafsan Tsaron Nijar Birgediya Janar Barmo ya bayyana jin daɗinsa game da ziyarar sannan ya sha alwashin sake haɗa kai da jami'an tsaron Nijeriya don magance matsalolin tsaron da ke addabar ƙasashen biyu.
A sanarwar bayan taron da wani babban jam'in sojin Nijar Kanar-Manjo Souleymane Moussa ya karanta, ya ce Nijar za ta duba yiwuwar sake haɗa kai da Nijeriya domin magance rashin tsaron da ke tsakaninsu.
Ƙasashen biyu sun daɗe suna fama da ƙalubalen tsaron sakamakon hare-haren mayaƙan Boko Haram waɗanda suka kashe dubban mutane tare da korar miliyoyi daga gidajensu.