A shekarar 2021 gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta nada AbdulRasheed Bawa a matsayin shugaban EFCC. Hoto/EFCC

Hukumar tsaro ta DSS a Nijeriya ta ce AbdulRasheed Bawa, shugaban hukumar EFCC mai yaki da cin hanci da rashawa da aka dakatar, yana hannunta.

Wata sanarwa da DSS ta wallafa a shafinta na Twitter jim kadan bayan shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da AbdulRasheed Bawa daga kan mukaminsa, ta ce "ya iso" ofishinta "awanni kadan da suka gabata."

Sanarwar da kakakin hukumar, Peter Afunanya ya sanya a hannu, ta kara da cewa an gayyaci AbdulRasheed Bawa don binciken da ake yi da ya shafe shi.

Tun da fari, wata sanarwa da ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayyar kasar ya fitar ranar Laraba ta ce an dakatar da Abdulrasheed Bawa domin samun damar gudanar da bincike a kan ofishinsa.

"Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da dakatar da Mr. AbdulRasheed Bawa a matsayin shugaban hukumar Economic and Financial Crimes Commission (EFCC) domin samun damar gudanar da binciken da ya dace kan ayyukan da ya yi lokacin da yake rike da ofishinsa," in ji sanarwar da Willie Bassey, daraktan watsa labarai na Sakataren Gwamnatin ya fitar.

An dauki matakin ne bayan manyan zarge-zargen da ake yi masa na amfani da ofishinsa ba bisa ka'ida ba, a cewar sanarwar.

An umarci AbdulRasheed Bawa ya mika harkokin ofishinsa cikin gaggawa ga daraktan gudanarwa na hukumar.

A shekarar 2021 gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta nada AbdulRasheed Bawa a matsayin shugaban EFCC wanda ya maye gurbin Umar Mohammed Abba, mutumin da ya rike mukamin shugaban riko na hukumar.

Shugaba Tinubu ya dakatar da Bawa ne kusan mako guda bayan ya dakatar da shugaban babban bankin Nijeriya Godwin Emefiele wanda daga bisani hukumar tsaro ta DSS ta kama shi.

TRT Afrika