Shugaban rundunar da ke tsaron shugaban Jamhuriyar Nijar Janar Abdourahamane Tchiani, ya ayyana kansa a matsayi sabon shugaban kasar.
Ya bayyana haka ne a wani jawabi da ya yi a gidan talabijin na kasar ranar Juma'a.
Janar Tchiani ya yi jawabi ne kana biyu bayan dakarun da ke tsaron Shugaba Mohamed Bazoum suka rufe fadar shugaban kasar da gidansa inda suka tsare shi.
Daga bisani wasu sojoji sun fito gidan talabijin inda suka ce sun yi wa shugaban kasar juyin mulki.
Amma wannan ne karo na farko da wani babban jami'in soji ya fito ya ayyana kansa a matsayin sabon shugaban kasar.
Janar Tchiani ya ce sun kifar da gwamnatin Bazoum ne sakamakon tabarbarewar tsaro da tattalin arziki a kasar.
Ya bukaci 'yan kasar su ba shi hadin kai domin fitar da su daga kangin da kasar ke ciki.
Takaitaccen bayani kan Janar Tchiani
Ba a san Janar Tchiani, wanda ke da shekara 62 a duniya ba, kafin tsohon shugaban Jamhuriyar Nijar Mahamadou Issoufou ya nada shi a matsayin shugaban rundunar da ke tsaron fadar shugaban kasa a 2011.
Issoufou ya nada A. Tchiani, kamar yadda ake kiransa, a mukamin Janar a 2018.
Bayanai sun ce mutum ne da ba ya son fitowa don nuna kansa amma jami'in sojin ne da abokan aikinsa ke matukar tsoronsa.
Ya ci gaba da aiki a matsayin shugaban rundunar da ke tsaron shugaban kasa har karshen wa'adin mulkin Mahamadou Issoufou 2021.