Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE) za ta janye daga Ƙungiyar Ƙasashe Masu Samar da Fetur ta Duniya, OPEC domin mayar da hankali kan "bukatun ƙasa", kamar yadda ta sanar, abin da ya jawo sabuwar girgiza yayin da farashin makamashi ke hauhawa saboda yakin Gabas ta Tsakiya.
UAE, ɗaya daga cikin manyan masu samar da mai a duniya, wadda a baya ta koka kan ƙa'idojin samarwa na OPEC, za ta janye a ranar Jumma'a, in ji wata sanarwa da kamfanin dillancin labarai na ƙasar, WAM ya ruwaito a ranar Talata.
"Wannan shawara tana nuna hangen nesa na dogon lokaci na UAE kan dabarun tattalin arziki da makomar makamashi," in ji bayanin UAE.
"A lokacin kasancewarmu a ƙungiyar, mun bayar da gudunmawa mai yawa har ma da ƙarin sadaukarwa don amfanin kowa," ta ƙara da cewa.
"Duk da haka, lokaci ya yi da za mu mayar da hankali kan abin da muradin ƙasa ya tanada."
Shin OPEC za ta raunana?
UAE ta kasance mamba ta OPEC ta hannun Masarautar Abu Dhabi tun 1967, shekaru huɗu ƙasar wadda a baya take ƙarƙshin kariyar Birtaniya ta zama ƙasa.
Matakin, wanda ya zo a yayin da ake fama da girgizar da aka samu a fannin mai mafi girma tun shekarun 1970, na iya raunana OPEC, wadda makwabciyar UAE, wato Saudiyya ke da rinjaye a ciki, kuma hakan na nufin zai ƙara girgiza kasuwannin mai na duniya, in ji masana.
Jigilolin mai na Gulf a halin yanzu suna fama saboda rufe Mashigar Hormuz da Iran ta yi, wacce ke wucewa kusa da UAE kuma ta nan ɗaya bisa biyar na man duniya ke wucewa.
UAE, wacce ta sha mummunan harin Iran, ta kuma fuskanci matsaloli a dangantakarta da Saudiya, babbar mai fitar da mai a duniya, bayan wani gagarumin rikici tsakanin ƙungiyoyin da kowace ƙasa ke goyon baya a Yemen.
'Kasuwar mai mai ƙarin rashin tabbas'
Kafin yakin, UAE ita ce ƙasa ta huɗu mafi samar da mai mai yawa a cikin ƙungiyar OPEC+ mai meabobi 22, bayan Saudiya, Rasha da Iraki.
Jorge Leon, wani masani a Rystad Energy, ya ce janyewar na iya rashin yin tasiri nan da nan a kasuwar mai yayin da jigilar ta Hormuz ke ci gaba da tsayawa.
Amma yanzu UAE za ta sami 'yanci ta ƙara yawan samarwa, "abin da ke haifar da tambayoyi game da dorewar matsayin Saudiyya a matsayin mai daidaita kasuwa -- kuma yana nuna yiwuwar kasuwar mai mai ƙarin rashin tabbas yayin da ikon OPEC na shimfida daidaito a samarwa ke raguwa."
Ikon sarrafa kasuwa
An kafa OPEC a 1960, kuma a 2016 ƙungiyar membobi 12 ta haɗa kai da wasu masu samar da mai 10 don kafa OPEC+ domin samun ƙarfi.
Kungiyar da ke Vienna ta ja hankalin duniya a 1973, lokacin da ta kakaba takunkumin mai kan kawancen Isra'ila a tsakiyar Yaƙin Yom Kippur, wanda ya haifar da rikicin mai na farko.
A cikin 'yan watanni kaɗan, farashinmai yaninka sau huɗu, abin da ya nuna karfin kungiyar.
Da fuskantar ƙarin masu fafatawa a shekarun 1980, ta gabatar da tsarin kaso (quota) wanda ya ba ta damar ƙara ikon sarrafa kasuwa.
Wannan dabarar ta sa ƙungiyar ta kasance cikin aminci a lokacin rikicin tattalin arziki na 2008 da girgizar farashi bayan annobar Covid-19, duk da ƙaruwar tashin hankali a ciki.










