| Hausa
DUNIYA
2 minti karatu
Fitaccen tsohon ɗanwasan Brazil Roberto Carlos ya musulunta - Rahotanni
Wani babban malami kuma jagora a Brazil Hammadeh, ya ce Carlos ya daɗe yana mu'amala da shi kuma ya ziyarce shi kimanin makonni huɗu da suka gabata, kuma a lokacin ne tsohon ɗanwasan ya furta kalmar shahada, ya rungumi Musulunci.
Fitaccen tsohon ɗanwasan Brazil Roberto Carlos ya musulunta - Rahotanni
Tsohon ɗanwasan Brazil Roberto Carlos lokacin da ya halarci wasan ƙarshe na Gasar Kofin Duniya tsakanin Argentina da Sifaniya a Amurka ranar 19/7/2026

Rahotanni na cewa fitaccen tsohon ɗanwasan ƙwallon ƙafa na Brazil kuma tsohon tauraron Real Madrid da Fenerbahçe Roberto Carlos ya musulunta a Brazil kimanin makonni huɗu da suka gabata, a cewar wani ɗan majalisar dokokin Turkiyya yana ambato wani fitaccen shugaban al'ummar Musulmi a Brazil.

Ali Şahin, ɗanmajalisa daga jam'iyyar AK mai mulkin Turkiyya ya bayyana haka bayan ganawa da wakilan al'ummar Musulmin Brazil a Sao Paulo.

Şahin ya ce ya ji labarin musuluntar Carlos daga bakin Sheikh Jihad Hammadeh, wani fitaccen jagora a cikin al'ummar Musulmin Brazil, wanda mmataimakin shugaba ne sannan mai ba da shawara kan addini a Kwamitin Fatawar Addini Musulunci ta Ƙasa (ANAJI).

A cewar Şahin, Hammadeh ya faɗa masa cewa Carlos ya daɗe yana mu'amala da shi kuma ya ziyarce shi kimanin makonni huɗu da suka gabata, lokacin da tsohon ɗanwasan ya furta kalmar shahada, sannan ya rungumi Musulunci.

Şahin ya sanar da hakan a wani rubutu da ya yi a shafukan sada zumunta bayan ganawa da Hammadeh da sauran wakilan al'ummar Musulmin Brazil a Cibiyar Ƙungiyar Matasa Masu Aikin Gudunmawa ta Musulunci ta Brazil da ke Sao Paulo.

Ya taya Carlos murna bisa yadda aka ruwaito ya rungumi Musulunci, kuma ya yi masa fatan zaman lafiya, da lafiya da wadata.

Wakilan kungiyoyin Musulmi da dama a Brazil sun halarci taron, ciki har da Shugaban Kungiyar Matasan Masu Aikin Gudunmawa ta Musulunci, Charif Neto, da Shugaban Gidauniyar Masallacin Pari, Omar Aref, da wakilan ANAJI da sauran kungiyoyin agaji da ilimi na Musulunci.

A baya bayan nan ne Roberto Carlos ya auri Suhayla At Tohiri, wata fitacciyar wakiliyar ƙwallon kafa 'yar asalin ƙasar Maroko da ke zaune a Sifaniya.

Ana daukar Carlos, mai shekaru 53, a matsayin ɗaya daga cikin manyan 'yanbaya a ɓangaren hagu a tarihin kwallon kafa. Dan Brazil ɗin ya shafe mafi yawan lokacinsa a Real Madrid kafin ya koma Fenerbahçe a Turkiyya a shekarar 2007.

Har kawo yanzu dai Carlos da kansa bai tabbatar da cewa ya musulunta a bainar jama'a ba.

Rumbun Labarai
Koriya ta Arewa ta yi alƙawarin kafa rundunar sojin ruwa mai amfani da makaman nukiliya
Faɗaɗa Yarjejeniyar Makka: Me Bangladesh za ta iya kawo wa ƙawancen?
Kotu a Las Vegas ta samu tsohon jagoran 'yandaba Duane 'Keffe D' Davis da laifi a kisan Tupac Shakur
Cizon sauron da suka shiga Jamus ta jirgin sama ya kashe ma'aikatan filin jirgi biyu
Tsananin zafi ya yi ajalin mutane 15,800 a Jamus a bazarar bana
Shugaban hukumar leƙen asiri ta Rasha ya tabbatar da ganawa da Shugaban CIA a Moscow
Ambaliya da zaftarewar ƙasa a Nepal sun yi ajalin gommai da ɓatar da ɗaruruwa a kusa da iyakar China
Trump ya gabatar da yarjejeniyar shekaru 30 ta haɗin gwiwar nukiliyar Saudiyya ga Majalisar Amurka
Mummunar guguwa ta katse wutar lantarki a gidaje 26,000 a kudu maso-gabashin Faransa
An kama mutane da dama bayan zanga-zangar ƙyamar Musulunci a Amurka
Fafaroma ya yi kira a kawo karshen cin zarafin da Isra'ila ke yi wa Falasdinawa a Gabar Yamma
CIA ta yi shakkar iƙirarin da Isra'ila ta yi kan shirin halaka Trump bayan taron NATO: rahoto
Za a fara shari'ar wanda ake zargi da hannu a kashe Tupac Shakur a Amurka
‘Yan Bangladesh akalla 16 sun mutu sakamakon gobara a masana'antar yin kujeru ta Saudiyya
Gobarar daji a jihar Washington ta Amurka ta tilasta wa dubban mutane tserewa
Jirgin yaƙin Amurka samfurin F-35 ya faɗi kusa da wani sansanin soji
Tarayyar Turai ta yi kira da a zartar da umarnin Kotun ICC na kamo Netanyahu
Macron ya ce Faransa na fama da gobarar daji mafi muni da ba a taɓa ganin irinta ba
Turai na babbakewa: Me muka sani zuwa yanzu?
Faransa da Sifaniya na fama da mummunar gobarar daji