Karshen ayyukan 'yan ta'addar PKK/YPG
GABAS TA TSAKIYA
9 minti karatu
Karshen ayyukan 'yan ta'addar PKK/YPGMatsin lambar soji daga Turkiyya, diflomasiyya da tuntuba sun taimaka wajen kassara manubar PKK/YPG. Rushewarta a yanzu na ba wa Ankara aiki mai wahala na mayar da ribar ayyukan soji zuwa zaman lafiya mai dorewa a yankin.
'Yan ta'addar PKK yayin taron ajje makamai a Qandil. (File photo/Reuters)

Rusa ƙta'addanci ta SDF da YPG ke jagoranta a Syria na iya zama wani muhimmin lokaci a cikin ƙoƙarin da Turkiyya ke yi na kawar da ta'addanci daga yankunanta da ma wajen sassan nata.

SDF, wadda YPG - reshen PKK da ke Syria ke mamaye da ita - ta sanar da wargaza kanta da kuma hadewa da sojojin Syria a farkon wannan makon.

PKK - wadda Turkiyya, Amurka, Tarayyar Turai da wasu ƙasashe da dama suka ayyana a matsayin ƙungiyar ta'addanci - da kuma ƙungiyoyin da ke da alaƙa da ita na da alhakin kashe-kashe da dama a Turkiyya da ma wasu sassanta.

Abubuwa da dama sun bai wa PKK damar ci gaba da tayar da ƙayar bayanta tsawon lokaci. Ikonta na aiki daga tsaunuka masu nisa, samun makamai da kuma iyakokin ayyukan soji na yau da kullum a irin wadannan wurare duk sun taimaka wajen dorewar ta.

Duk da haka, cigaban da ya faru a wajen fagen daga na iya zama mafi muhimmanci wajen bai wa kungiyar damar ci gaba da ayyukan ta'addanci.

Wani muhimmin abu shi ne shigar ƙungiyoyin siyasa masu goyon bayan PKK a cikin tsarin siyasar Turkiyya. A babban zaɓen watan Yunin 2015, HDP mai alaƙa da PKK ta lashe kashi 13.12 cikin ɗari na ƙuri'un, wanda ya zarce kashi 10 cikin ɗari na ƙa'idar samun kujeru a majalisa.

An danganta sakamakon da wani ɓangare da goyon bayan da aka samu daga masu zaɓe 'yan asalin Kurdawa da kuma wasu masu zaɓe 'yan ta more da masu kishin addini waɗanda suka yi adawa da Jam'iyyar Adalci da Ci Gaba mai mulki (AKP).

Ƙarfin da ba zato ba tsammani ya nuna cewa ya yi tasiri ga lissafin shugabannin PKK a wani lokaci mai muhimmanci.

A lokacin, an fara wani zaman lafiya tsakanin Ankara da ƙungiyar tun daga 2013, inda ake tattaunawa kan kwance damar makamai. Amma maimakon barin gwagwarmayar makamai, PKK ta ci gaba da ayyukanta.

Abubuwan da suka faru a Syria daga baya sun haifar da wata dama. Yaƙin basasa da rugujewar ikon gwamnati a sassan arewacin Syria sun ba wa YPG damar mamayewa da kuma kafa iko a manyan yankuna.

Da bayyanar Daesh, YPG ta zama muhimmiyar abokiyar hulɗa ga Washington a yaƙi da ƙungiyar ta'addancin.

YPG tana aiki a ƙarƙashin babbar ƙungiyar SDF, inda ta sami tallafin sojojin Amurka da tallafin jiragen sama, kuma daga ƙarshe ta sami iko a kan wani yanki mai yawa na arewa maso-gabashin Syria.

Duk da haka, wannan shirin a yanzu ya zo karshe.

Me ya sa PKK ta ruguje?

Sabbin abubuwan da suka faru suna da alaƙa da tsarin rushewar PKK.

A watan Fabrairun 2025, shugaban ƙungiyar ta'addanci da aka tsare, Abdullah Ocalan, ya yi kira ga PKK da ta kwance damarar yaƙi ta kuma wargaje.

Ci gaban siyasa da na dokoki da suka biyo baya a Turkiyya sun samar da tsarin da 'yan bindiga za su miƙa makamansu su kuma sake shiga cikin rayuwar farar hula.

Rahotannin sun nuna cewa hukumomin Turkiyya da na Iraki suna sa ido kan tsarin kwance damarar.

Wannan shawara ba ta fito a ware ba. Tsawon shekaru, Ankara ta bi PKK ta hanyar haɗa matsin lamba na soja da diflomasiyya, gami da bi ta kan ƙungiyoyin da ke da alaƙa da ita a Syria da Iraki.

Turkiyya ta yi adawa da shawarar Washington na yin haɗin gwiwa da YPG, tana mai jayayya da cewa wata ƙungiya da Ankara ta ɗauka a matsayin ƙungiyar ta'addanci ba za ta iya zama wata hanya mai tasiri ta kawar da wata ƙungiyar ta'addanci ba, wato Daesh.

Duk da ayyukan diflomasiyya, gami da takaddama kan samar da makamai da tashin hankali da ƙawayenta na NATO, Turkiyya ta ci gaba da gangamin yaƙi da ta'addanci a kan PKK da YPG.

Ankara ta kuma gudanar da ayyukan soji a arewacin Syria da Iraki da dama, wanda hakan ya rage wa kungiyoyin 'yancin walwala sosai.

Ci gaban da aka samu a Syria daga baya ya ƙara canza tsarin dabarun yaƙin.

Bayan faduwar shugaban kama-karya Bashar Al Assad a watan Disamban 2024, daidaiton iko a Syria ya canza sosai.

Fitowar sabuwar gwamnati, tare da goyon bayan Turkiyya ga Damascus, ya haifar da yanayi wanda YPG ba za ta iya dogaro da irin matakin kariyar Amurka ba.

YPG ta yi tsammanin goyon bayan Washington zai ci gaba.

Duk da haka, kusancin da shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ke da shi da Shugaba Donald Trump, tare da shawarar Amurka na rage yawan sojojinta a Syria, ya canza waɗannan lissafin.

Turkiyya ta kuma nuna shirinta na tallafawa gwamnatin Syria ta hanyar soji idan ya zama dole. Ganin yadda take fuskantar barazanar fuskantar gwamnatin Syia wacce Turkiyya ke marawa baya, YPG tana da iyakantaccen zaɓi.

Fagen daga ya riga ya sauya

Duk da cewa matsayin YPG ya tabarbare a Syria, PKK da kanta ta riga ta fuskanci koma baya sosai.

Tun daga tsakiyar shekarun 2010, Turkiyya ta ƙara dogaro da jiragen sama marasa matuki (UAVs) don kai hari kan cibiyoyi da kwamandojin PKK.

Gabatar da jiragen sama marasa matuki ya canza yanayin rikicin sosai. 'Yan ta'addar PKK sun ƙara janyewa daga yankin Turkiyya suka inda nemi mafaka a yankunan tsaunuka na arewacin Iraki, wajen da suka yi ƙoƙarin buya daga gano si da kai musu hari.

Tasirin ya yi yawa. Hare-haren ta'addanci na PKK a cikin Turkiyya sun ragu sosai, yayin da ikon rundunar na aiki a bayyane ya ragu sosai. 

A tsawon lokaci, ƙungiyar ta sami kanta da ƙarancin zaɓi na ayyukan soji. Ko da ba tare da an kwance damarar yaƙi a hukumance ba, an rage mata hanyoyin da za ta bi inda ta koma yin aiki daga kogo da wuraren da ke ƙarƙashin ƙasa.

A wannan gaba, za a iya fahimtar tsarin wargajewar ba kawai a matsayin shawara ta siyasa ba, har ma a matsayin sakamakon sauyi na asali a daidaiton soji.

Duk da haka, wannan ci gaban ya haifar da muhawara a cikin Turkiyya, musamman tsakanin waɗanda ke adawa da tattaunawa da ƙungiyar ta'addanci ta PKK.

Hujjarsu a bayyane take: idan an riga an kawar da ƙungiyar ta hanyar soja, me ya sa gwamnati za ta shiga tattaunawa da ita?

Amsar gwamnati ta dogara ne akan bambanci tsakanin nasara kan ƙungiya mai makamai da warware manyan sakamakon zamantakewa da siyasa na shekaru da yawa na rikici.

Kawancen gwamnati, ƙarƙashin jagorancin Jam'iyyar AK da Jam'iyyar MHP da ‘yan kishin kasa, ya jaddada ƙarfafa haɗin kai tsakanin 'yan asalin Turkiyya da Kurdawa na Turkiyya.

Daga wannan mahangar, manufar ba wai kawai ita ce a kayar da PKK ba, har ma a tabbatar da cewa Kurdawa ba su ɗauki ƙarshen rikicin a matsayin shan kaye a kansu ba.

Saboda haka, sulhu mai ɗorewa yana buƙatar fiye da nasarar soji. Yana buƙatar hana ƙiyayya da tashin hankali ya haifar da kuma hana zama tushen rarrabuwar kawuna na dindindin.

Ba wa 'yan bindiga damar kwance damarar makamai, kuma inda doka ta tanada, komawa rayuwar farar hula za a iya ɗaukar hakan a matsayin wani ɓangare na wannan dabarar.

Daga nasarar soji zuwa fagen siyasa

A wata mahangar ta daban, kusan dukkan masu ruwa da tsaki a cikin wannan tsari za su amfana daga rusa PKK.

Turkiyya za ta iya kawo ƙarshen yakin ta'addanci na tsawon shekaru da dama. Syria da Iraki za su iya amfana daga kwanciyar hankali mafi girma a yankunansu, yayin da al'ummomin Kurdawa za su iya amfana daga raguwar tashin hankali da kuma yiwuwar makomar siyasa ba tare da wata ƙungiyar 'yan aware masu ɗauke da makamai ba.

Amma ba kowane mai taka rawa a yankin ne ya yi murna da wannan sakamakon ba.

Musamman Isra'ila, a tarihi, ta ɗauki ƙungiyoyin Kurdawa a matsayin abokan hulɗa don kalubalantar ƙasashe kamar Turkiyya da Syria.

Ma'anar ta kasance mai sauƙi: ƙungiyoyin da ke adawa da waɗannan gwamnatocin za su iya zama masu amfani a gare su.

Duk da cewa damar amfani da PKK a kan Turkiyya ta riga ta ragu, YPG ta zama abokiyar tarayya mai muhimmanci a cikin yanayin Syria bayan kawar da Assad.

Duk da haka, Ankara ta nemi hana wannan yanayin ta hanyar haɗa matakan soji, diflomasiyya da siyasa.

Turkiyya ta goyi bayan gwamnatin Syria, ta yi aiki tare da Washington don rage goyon bayan da take bai wa YPG, kuma, wataƙila mafi muhimmanci, ta goyi bayan shigar da ƙungiyar cikin cibiyoyin gwamnatin Syria.

Manufar ita ce shawo kan ƙungiyar ta shiga cikin sabbin tsare-tsaren siyasa da tsaro na Syria, maimakon neman 'yancin kai na dindindin.

Saboda haka Isra'ila ta gaza mayar da YPG matsayin madadin irin rawar da Amurka ta taka a baya.

Wannan ba yana nufin cewa Isra'ila ta janye daga Syria ba. Kasancewar sojojinta a wasu sassan kudancin Syria da kuma dangantakarta da al'ummar Druze sun kasance muhimman abubuwa na daidaiton yankin da ke ci gaba.

Ga Damascus, duk da haka, yiwuwar warware matsalar Kurdawa tare da goyon bayan Turkiyya na wakiltar babbar nasarar dabarun.

Saboda da haka, wargaza PKK/YPG na iya zama wani muhimmin cigaba da ya wuce iyakokin Turkiyya.

Matsin lamba na soja, diflomasiyya da shiga harkokin siyasa na Ankara ya rage wa ƙungiyar damar yin aiki a Turkiyya, Iraki da Syria.

Idan aka kammala aikin cikin nasara, sakamakon zai iya wuce ƙarshen yakin ta'addanci na PKK nan take.

Turkiyya za ta iya fitowa daga rikicin shekaru arba'in da suka gabata tare da dangantaka mai dorewa tsakanin Turkiyya da Kurdawa, yayin da Syria da Iraki za su iya amfana daga kawar da wani babban mai fafutukar kare haƙƙin jama'a wanda ba shi da gwamnati.

Mafi girman muhimmanci shi ne ƙarshen PKK/YPG na iya nuna cewa nasarar soja kaɗai ba ta isa ta cim ma zaman lafiya mai ɗore wa ba.

Kalubalen Ankara yanzu shi ne mayar da shan kayen soja na ƙungiyar zuwa sulhu mai ɗore wa na siyasa - wanda ke raba al'ummar Kurdawa na ƙasar da yakin ta'addanci da ta yi iƙirarin su take wakilta.

Idan aka yi nasara, wargajewar PKK/YPG za ta iya zama fiye da kawo ƙarshen gangamin yaki da ta'addanci.

Zai iya zama farkon sabon lokacin kwanciyar hankali a faɗin Turkiyya, Syria da Iraki, tare da yiwuwar fa'ida ga Iran da Gabas ta Tsakiya baki ɗaya.