| Hausa
GABAS TA TSAKIYA
2 minti karatu
Netanyahu na Isra'ila ya yi tattaunawar sirri a UAE da Al Nahyan yayin yaƙin Iran
Sanarwar daga Tel Aviv na zuwa ne kwana ɗaya bayan jakadan Amurka Mike Huckabee ya ce Isra'ila ta tura tsare-tsaren tsaron sararrin samaniya da jami'ai zuwa Haɗaɗɗaiyar Dalar Larabawa (UAE) a lokacin yaƙi da Iran.
Netanyahu na Isra'ila ya yi tattaunawar sirri a UAE da Al Nahyan yayin yaƙin Iran
GAnawar ta janyo wata "mafita mai cike da tarihi" a dangantaka tsakanin Isra'ila da Haɗaɗɗiyar daular Larabawa, in ji sanarwar. / Reuters

Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya yi tattaunawar "sirri" da shugaban ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa yayin yaƙin Iran.

"A lokacin aikin 'Lion's Roar', Firaminista Benjamin Netanyahu ya kai wata ziyarar sirri Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE), inda ya gana da Shugaban UAE Sheikh Mohammed bin Zayed Al Nahyan," kamar yadda ofishinsa ya bayyana a wata sanarwa ranar Laraba.

Sanarwar na zuwa ne kwana ɗaya bayan jakadan Amurka a Isra’ila Mike Huckabee ya bayyana cewa Isra’ila ta tura tsare-tsaren tsaron sararin samaniyarta da jami’ai da za su sarrafa su zuwa UAE yayin yaƙi da Iran.

Yayin da yake tabbatar da kalaman Huckabee, ofishin Netanyahu ya ce ziyarar "wata muhimmiyar nasara mai cike da tarihi ce a dangantaka tsakanin Isra’ila da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa."

Ramuwar gayya kan hare-haren Amurka da Isra’ila

Tehran ta kai hare-hare Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa fiye da ko wace ƙasa a lokacin yaƙin da Amurka da Isra’ila suka ƙaadamar a Iran a ƙarshen watan Fabrairu.

Duk da wata yarjejeniyar tsagaita wuta da ta fara aiki a watan da ya gabata, Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa ta ba da rahoton hare-haren makamai masu linzami da na jirage marasa matuƙa daga Iran.

Ƙasar Haɗaɗɗira Daular Larabawa, mai arzikin mai, wata babbar ƙawar Amurka ce a yankin kuma tana cikin ƙasashen Larabawa da ke da dangantaka a hukumance da Isra’ila bayan rattaba hannu a yarjejeniyar Abraham Accords a lokacin wa’adin mulkin Shugaban Amurka Donald Trump na farko a shekarar 2020.