| Hausa
TURKIYYA
1 minti karatu
Ministan Harkokin Wajen Masar ya gode wa Turkiyya saboda tarban karamci da ta yi wa Mohamed Salah
Abdelatty ya ce, an gina dangantakar da ke tsakanin Turkiyya da Masar "bisa ginshiƙi mai ƙarfi".
Ministan Harkokin Wajen Masar ya gode wa Turkiyya saboda tarban karamci da ta yi wa Mohamed Salah
Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan ya gana da takwaransa na Masar Badr Abdelatty a El Alamein a ranar 13 ga Agusta, 2026

Ministan Harkokin Wajen Masar Badr Abdelatty ya gode wa al'ummar Turkiyya saboda "tarba da suka yi wa ɗanwasan Masar Mohamed Salah ta karamci,” wanda ya koma ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Trabzonspor a ƙasar kwanan nan.

"Muna godiya ga al'ummar Turkiyya saboda kyakkyawar tarbar da aka yi wa fitaccen ɗanwasanmu Mohamed Salah wanda ya dawo ƙungiyar Trabzonspor, mun ji ɗaɗai sosai," in ji Abdelatty a ranar Alhamis a wani taron manema labarai na haɗin gwiwa da Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan.

Fidan ya kai ziyarar aiki a Masar.

Abdelatty ya ce, an gina dangantakar da ke tsakanin Turkiyya da Masar "bisa ginshiƙi mai ƙarfi".

"Muna Allah wadai da duk wani hari da Isra'ila ke kai wa Siriya," in ji shi.

Abdelatty ya kuma ce Masar ta "yarda" da Turkiyya ɗari bisa ɗari a kan tallafa wa haƙƙin ikon yankin Sudan kan ta yi fatali da duk wani shiri na rabuwar ƙasar.

Kan batun Gaza kuwa, ya ce: "Ƙungiyoyin Falasɗinawa a Gaza sun mayar da martani yadda ya kamata wajen ajiye makamansu da komawa tsarin siyasa. Kuma dole ne Isra'ila ita ma ta sauke nauyin da ta rataya a wuyanta."