| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
Dakarun Nijeriya sun ce manyan kwamandojin DAESH sun miƙa wuya sakamakon ƙara matsin lambar soji
Rundunar ta ce ana tsare da waɗanda suka miƙa wuya a wani wuri mai tsaro, inda ake tantance su, yi musu tambayoyi da kuma gudanar da sauran matakan da suka dace bisa ƙa'idojin aikin soji.
Dakarun Nijeriya sun ce manyan kwamandojin DAESH sun miƙa wuya sakamakon ƙara matsin lambar soji
Kwamandojin DAESH sun miƙa wuya ga sojojin Nijeriya. / Nigerian army

Sojojin Nijeriya sun ce wani sabon rukuni na manyan kwamandojin ƙungiyar DAESH sun miƙa wuya ga dakarunsu a yankin arewa maso gabashin ƙasar, bayan da aka ƙara ƙaimi wajen gudanar da ayyukan yaƙi da ta'addanci.

A cikin wata sanarwa da Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa Maso Gabas, Operation HADIN KAI, ta fitar a ranar Lahadi, ta ce waɗanda ake zargin jagororin 'yanta'addan ne sun bar maboyarsu sakamakon ci gaba da farmakin sojoji da kuma bayanan sirri da rundunar ta bayyana a matsayin ingantattu kuma masu amfani.

Rundunar ta ce ana tsare da waɗanda suka miƙa wuya a wani wuri mai tsaro, inda ake tantance su, yi musu tambayoyi da kuma gudanar da sauran matakan da suka dace bisa ƙa'idojin aikin soji.

A cewar Operation HADIN KAI, wannan ci gaban na nuna tasirin hare-haren da sojoji ke ci gaba da kaiwa domin rusa sansanonin 'yanta'adda, tarwatsa tsarin jagorancinsu da kuma katse hanyoyin samar musu da kayan aiki a faɗin yankin arewa maso gabas.

Rundunar ta kuma ce a cikin makon da ya gabata kaɗai, mayaƙan da ake zargin 'yanta'adda su 76 tare da wasu daga cikin iyalansu sun miƙa wuya ga dakarun soji.

Jami'an sojin sun danganta yawaitar miƙa wuya da matsin lambar da ake ci gaba da yi ta hanyar haɗa kai tsakanin hukumomin tsaro, amfani da bayanan sirri da kuma kai hare-hare kan 'yanta'addan.

Operation HADIN KAI ta ce za ta ci gaba da kai farmaki kan ƙungiyoyin Boko Haram da DAESH har sai an kawar da sauran mayaƙansu ko kuma sun miƙa wuya.

A cikin 'yan shekarun nan, sojojin Nijeriya sun sha sanar da miƙa wuya da ɗaruruwan waɗanda ake zargin 'yantawaye ne a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarinsu na kawo ƙarshen rikicin da ya daɗe yana addabar yankin arewa maso gabashin ƙasar.