Babban kwamandan Amurka a Turai ya gargaɗi ma’ikatar tsaron Amurka Pentagon a asirce cewa ba shi da isassun dakarun ruwa na ci gaba da kare Isra’ila daga hare-haren makamai masu linzami, kamar yadda jaridar The Washington Post ta ruwaito ranar Asabar.
Janar Alexus Grynkewich, shugaban rundunar sojin Amurka a Turai, ya shaida wa manyan jami’an Pentagon cewa idan ba a samar da ƙarin jirgin ruwa na yaƙi (Navy destroyer a Ingilishi) ba, zai zama wajibi ya fifita kare ‘gidan’ Amurka kan Isra’ila, in ji jami’ai.
Wani jami’in ma’aikatar tsaron Amurka ya ce gargaɗin ya biyo bayan wata ɗab’ia ta al’ada ne inda manyan kwamandoji ke jan hankalin ma’aikatar tsaro ta Pentagon a lokacin da ƙarancin kayayyaki ke haddasa barazana ga aiki yayin da suke gogayya wajen buƙatar ƙayyadaddun dakaru da makamai.
Gagarɗin na zuwa ne yayin da yaƙi na watanni biyar ke ƙara zafi bayan tattaunawar sulhu tsakanin Washington da Tehran ta rushe, inda rahotanni suka ce hare-hare babu ƙaƙƙautawa na ƙararar da makaman kariyar Amurka.
Matsin sojin ruwa na ƙaruwa
Sojin ruwan ƙasar ta fuskanci ƙarin matsi yayin da gwamnatin Trump ta ba da umarnin yi wa Iran ƙawanya biyo bayan matakin da Tehran ta ɗauka na rufe mashigar Hormuz, lamarin da ya katse jigilar mai da kasuwancin duniya.
Jiragen yaƙin ruwan Amurka a gabashin tekun meditareiniyan sun daɗe suna taimakawa wajen kare Isra’ilal, inda suke amfani da ingatattun na’urar hango ababe da tsare-tsaren makamai masu linzami wajen kakkaɓo makamai masu linzamin da Iran da ‘yan Houthi na Yemen suka harbo.
Rundunar sojin Amurka a Turai ita take jagorantar waɗannan ayyukan yayin da take tabbatar da kasancewa cikin shiri kan yiwuwar barazana daga Rasha kan wani wuri na ƙawancen tsaron NATO.
Sojin ruwan Amurkan na amfani da jiragen yaƙi na ruwa biyar daga Rota, a Sifaniya inda ake tsammanin na shidan daga baya cikin wannan shekarar. Sai dai kuma, jami’ai sun ce yanayin tafiyar yaƙin Amurka kan Iran ya haifar da ƙalubale na tabbatar da gyara su, lamarin da ke rage samuwar jiragen ruwan.

















