Mataimakin shugaban Nijeriya, Kashim Shettima, ya roƙi al’ummar arewacin ƙasar da kada su yi fargabar sake zaɓen Shugaba Bola Tinubu a shekarar 2027, yana mai cewa yankin ya amfana da manufofi da ayyukan raya ƙasa na gwamnatin.
Shettima ya yi wannan roƙo ne a ranar Litinin lokacin da ya karɓi baƙuncin wata tawaga daga ƙungiyar Arewa for Asiwaju (A4A), wadda ke gudanar da yaƙin neman sake zaɓen Tinubu, a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.
Ya buƙaci shugabannin siyasa da al’ummar Arewa su haɗa kai wajen mara wa shugaban ƙasar baya, yana mai cewa ci-gaban yankin da walwalar al’ummarsa na daga cikin muhimman abubuwan da gwamnatin ke bai wa fifiko.
A cewar Shettima, Arewa ta amfana da naɗe-naɗen muƙaman gwamnati da tallafin noma da manyan ayyukan more rayuwa da ake gudanarwa a ƙasar.
Ya bayar da misali da cewa, “Bankin Noma na Nijeriya ya raba naira biliyan 450 ga ƙananan manoma 700,000 a faɗin ƙasar,” inda ya ce kusan kashi 70 cikin 100 na waɗanda suka amfana ‘yan Arewa ne.

“Shugaban ƙasa yana son Arewa, kuma zai yi aiki domin ci-gaban Arewa,” in ji Shettima, inda ya buƙaci ƙungiyar ta ƙara ƙaimi wajen wayar da kan jama’a a unguwanni da ƙananan hukumomi da sauran al’ummomin yankin.
‘Yan adawa na shirye-shiryen zaɓen 2027
Wannan kira na zuwa ne a daidai lokacin da jam’iyyun siyasa ke shirye-shiryen kayar da Tinubu a babban zaɓe a Nijeriya na shekarar 2027.
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta tsara gudanar da zaben shugaban ƙasa da na ‘yan majalisar dokoki a ranar 16 ga Janairu, 2027, yayin da za a gudanar da zaɓen gwamnoni da na ‘yan majalisun dokokin jihohi a ranar 6 ga Fabrairu, 2027.
Tinubu, na jam’iyyar APC mai mulki, na neman yin ta-zarce, tare da Shettima a matsayin mataimakinsa.
Daga cikin ‘yan takarar adawa akwai tsohon mataimakin shugaban ƙasar, Atiku Abubakar, wanda shi ne ɗantakarar shugaban ƙasa na jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), da kuma tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi, wanda ke takara a ƙarƙashin jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC).
Alƙawarin ƙungiyar na ƙarfafa yaƙin neman zaɓe
Tun da farko, tsohon gwamnan jihar Jigawa, Abubakar Badaru, wanda shi ne darakta-janar na ƙungiyar, ya ce A4A za ta ci gaba da tuntuɓar shugabannin siyasa da na addini domin samun goyon bayansu ga tikitin Tinubu da Shettima a zaɓen 2027.
Badaru ya ce ƙungiyar ta gudanar da tarurruka da manyan mutane masu ruwa da tsaki, kuma tana shirin ƙara tattaunawa da malaman addinin Musulunci da na Kirista.
Ya ƙara da cewa ƙungiyar tana aiki tare da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa domin ƙarfafa samun goyon baya daga tushe, tare da taimakawa sauran manyan tsare-tsaren yaƙin neman zaɓen.
Shi ma tsohon gwamnan jihar Kano, Ibrahim Shekarau, wanda shi ne shugaban kwamitin amintattu na ƙungiyar, ya ce A4A na shirin maimaita nasarar da ta samu wajen tallafa wa Tinubu a zaben shugaban ƙasa na shekarar 2023.
Shekarau ya ce ƙungiyar ta dade tana tattaunawa da gwamnonin Arewa da sauran masu ruwa da tsaki domin ƙarfafa haɗin kai gabanin zaɓe mai zuwa.
Ya kuma bayyana cewa ƙungiyar na shirin kafa babbar sakatariya ta dindindin domin daidaita ayyukanta, da sa ido kan rahotannin masu kula da jihohi da kuma tsara yadda za a gudanar da ayyukan wayar da kan jama’a.
Kazalika ƙungiyar ta gayyaci Shettima domin ƙaddamar da sabon ofishinta a ranar 17 ga Oktoba, 2027.
Taron ya samu halartar tsoffin gwamnoni da dama, ciki har da Joshua Dariye da Simon Lalong na jihar Filato, da Jolly Nyame na jihar Taraba, da Yahaya Bello na jihar Kogi, da Ibrahim Shehu Shema na jihar Katsina da kuma Isa Yuguda na jihar Bauchi.
Sauran mahalarta sun haɗa da mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan manufofi da daidaita ayyuka, Hadiza Bala Usman, da shugaban Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Nijeriya (NDLEA), Buba Marwa.





















