Ƙungiyar Agaji ta Red Crescent ta Iran ta ce mutane huɗu, ciki har da yaro ɗaya, sun mutu, sannan fiye da mutane 50 sun jikkata sakamakon harin Amurka yayin da suke halartar wani taron bikin aure a yankin kudancin ƙasar.
"Harin makami mai linzami na Amurka ya afka kan wani gida a birnin Kuhestak, a gundumar Sirik ta lardin Hormozgan, inda ake gudanar da bikin aure," in ji wani sako da Red Crescent ta wallafa a shafinta na X a safiyar ranar Laraba.
"Fiye da mutane 50 sun jikkata, sannan wasu mutane huɗu, ciki har da wani ƙaramin yaro, sun yi shahada."
Wani bidiyo da wani shafin gwamnatin Iran ya wallafa ya nuna tarkace da ɓarna mai yawa a wurin da aka ce wajen daurin auren ne a Sirik bayan harin Amurka, inda aka ji mutane suna ta koke-koke.
Ko da yake hukumomin Amurka ba su tabbatar da labarin ba tukuna.
Tun da farko, Mataimakin Gwamnan Lardin Hormozgan da ke kudancin ƙasar, Ahmad Nafisi, ya shaida wa gidan talabijin na gwamnatin kasar cewa: "Mutane biyu sun yi shahada, wasu kuma sun jikkata."
Gudumar kudancin Sirik na kan hanyar Mashigar Teku na Hormuz.
Amurka ta ce tana kai hare-hare kan wuraren da dakarun kare juyin juya halin Iran ke kai hari bayan "yunkurin kai hare-hare na baya-bayan nan ... kan jiragen ruwa na kasuwanci a mashigar tekun Hormuz da kuma kan sojojin Amurka da aka tura yankin".
A ranar Talata, kafofin watsa labarai na Iran sun ba da rahoton fashewar abubuwa a birane da dama a gabashin yankin Hormuz da kuma wani filin jirgin sama da ke kudancin lardin Kerman.
Amurka ta haɗa ƙarfi da Isra'ila wajen kai hare-hare kan Iran tun daga ranar 28 ga Fabrairu, inda suka kashe tsohon Jagoran Addini na Ƙasar, Ali Khamenei, da sauran manyan jami'an gwamnati da kuma ɗaruruwan fararen hula.
Cikin sauri Iran ta mayar da martani ta hanyar karbe iko da Mashigar Tekun Hormuz, wata muhimmiyar hanya da ake bi da kashi ɗaya bisa biyar na man fetur da duniya ke amfani da shi, sannan ta yi ta ruwan makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuƙa a ƙasashen yankin Tekun Fasha.
Da farko, an ɗauki kusan kwanaki 40 Amurka da Isra'ila suna kai munanan hare-hare akai-akai galibi a kusa da Hormuz, wanda hakan ya rage damar cim ma yarjejeniyar zaman lafiya ta ƙarshe.





















