Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya karɓi Ministan Tsaro, Janar Christopher Gwabin Musa (mai ritaya), a gidan Shugaban Ƙasa na Legas, inda suka duba tsarin tsaron ƙasa da kariyar Nijeriya.
Tattaunawar ta mayar da hankali kan ayyukan da ake ci gaba da gudanarwa na yaƙi da ta’addanci da ’yanbindiga, buƙatun da ake da su a fagen daga, da kuma dabarun haɗin gwiwar hukumomin tsaro.
Mataimakiyar musamman ta Ministan Tsaro kan harkokin yaɗa labarai, Leah Katung-Babatunde, ce ta bayyana hakan cikin wata sanarwa.
Taron ya kuma duba shirye-shiryen tsaro da ake aiwatarwa da kuma sauye-sauyen da aka gabatar da nufin “ƙarfafa gwiwar sojoji, zamanantar da kayan aikin soji da inganta kayayyakin more rayuwar sojoji a faɗin ƙasar.”
Shugaba Tinubu ya bayyana gamsuwarsa da ci gaban da aka samu wajen kare al’ummomin da ke cikin haɗari, tare da sake tabbatar da aniyar gwamnatinsa na ci gaba da tallafa wa Ma’aikatar Tsaro.
Janar Musa ya yi wa shugaban ƙasa bayani kan shirye-shiryen tsaro da ake aiwatarwa, dabarun samar da kayayyakin aiki da kuma sauye-sauyen da aka gabatar.
Ya kuma gode wa shugaban ƙasa kan ci gaba da jagoranci da goyon bayan da yake bai wa hukumomin tsaron Nijeriya.
Ministan ya tabbatar da cewa Ma’aikatar Tsaro za ta ci gaba da gudanar da aikinta da ƙuduri da riƙon amana.



















