Kungiyar Lafiya ta Duniya a ranar Litinin ta ce babu bukatar a firgita kuma babu hatsari sosai ga lafiyar jama’a bayan mutane uku sun mutu sakamakon kamuwa da cutar hantavirus da beraye ke yadawa a cikin wani babban jirgin ruwa a Tekun Atlantika.
Tawagar Matafiya a Teku ta Holland ta ce tana ‘kokarin shawo kan mummunan yanayin lafiya’ a wani babban jirgin ruwan yawon bude ido a kusuwar duniya MV Hondius, wanda ya isa gabar Cabo Verde, wani tsibiri da ke gab da gabar tekun Yammacin Afirka.
Jirgin ruwan ya bar Ajantina kimanin makonni uku da suka gabata dauke da fasinjoji kimanin 150 kuma ya tsaya a Antaktika da sauran wurare a yayin da yake hanyar Cabo Verde, kamar yadda rahotannin kafafen watsa labarai suka bayyana.
“Babu hatsari sosai ga jama’a baki daya. Babu bukatar a firgita ko hana zirga-zirga. in ji wata sanarwa da dataktan WHO na TUrai, Hans Kluge ya fitar.
Holland ta tabbatar da mutuwar ‘yan kasarta
Kluge ya ce WHO tana aiki cikin gaggawa don tallafawa agajin da aka bayar ga barkewar cutar tare da yin aiki tare da ƙasashen da abin ya shafa don tallafa wa kula da lafiya, kwashe mutane, bincike da kuma tantance hatsarin lafiyar jama'a.
"Kamuwa da cutar Hantavirus ba kasafai ake samun sa ba kuma galibi yana da alaƙa da cudanya da beraye masu dauke da cutar. Duk da cewa tana da tsanani a wasu lokuta, ba a iya yaɗa ta cikin sauƙi tsakanin mutane," in ji Kluge.
Mai magana da yawun Ma'aikatar Harkokin Wajen Holland ya tabbatar da cewa fasinjoji biyu ‘yan kasar Holland sun mutu amma bai ba da ƙarin bayani ba. Mutum na uku da ya mutu ɗan ƙasar Jamus ne.
A cikin wani rubutu ta shafin X WHO ta bayyana cewa ɗaya daga cikin fasinjojin da ba su da lafiya yana cikin mawuyacin hali kuma yana samun kulawa a Afirka ta Kudu.
Sky News ta ruwaito cewa fasinjan ɗan Birtaniya ne, tana mai rawaito Ma'aikatar Lafiya ta Afirka ta Kudu.
Gwaje-gwajen dakin bincike sun tabbatar da cewa cutar hantavirus ta bulla ta kama daya daga cikin mutane shida, in ji ƙungiyar.









