Kasashen Afirka da ba su da tsofaffin shugabanni masu rai
AFIRKA
4 minti karatu
Kasashen Afirka da ba su da tsofaffin shugabanni masu raiNijeriya na da tsaffin shuwagabannin kasa da ke raye, daidaidai har guda biyar, amma kasa kamar Kamaru, ba ta da ko da tsohon shugaban kasa guda a duniya a yau, duk da cewa shekara daya kasashen suka samu ‘yancin-kai?
Kasashen Afirka da ba su da tsofaffin shugabanni masu rai

Nijeriya na da tsaffin shuwagabannin kasa da ke raye, daidaidai har guda biyar,
amma kasa kamar Kamaru, ba ta da ko da tsohon shugaban kasa guda a duniya a
yau, duk da cewa shekara daya kasashen suka samu ‘yancin-kai?

A duk fadin Afirka, akwai irin wadannan misalan. To me ya sa haka, kuma ya
hakan yake tasiri kan siyasa da cigaban kasa?

Kasar Kamaru ta samu ’yancin kai ne a shekarar 1960, amma fa shekaru 66 bayan
nan, shugabanni biyu kacal ta taba yi.

Shugaba Ahmadou Ahidjo ya jagoranci kasar daga 1960 zuwa 1982, lokacin da
Paul Biya ya karbe mulki. Sannan tun a 1989, Ahidjo ya bar duniya.

Haka lamarin yake a kasar Equatorial Guinea. Tun bayan samun ’yancin kanta a
shekarar 1968, shugabanni biyu kacal ta taba yi.

Shugaba Teodoro Obiang da ke mulkin kasar a yau ya kwace mulki a shekarar
1979, daga kawunsa, Francisco Macías Nguema, wanda aka kashe ta hanyar
hukuncin kisa.

Shugaba Salva Kiir ne ke jagorantar Sudan ta Kudu a yau, tun bayan da kasar ta
samu ’yancin-kai a shekarar 2011. Kenan Sudan ta Kudu shugaba daya ta taba yi
cikin shekara 15 da samuwarta.

Irin wannan labarin ne kuma ya faru a kasar Eritrea, wadda ta samu ’yancin kai a
shekarar 1993. Isaias Afwerki ne shugaban kasar tun daga ranar farko, har zuwa
yau.

Sannan akwai kasar Zambiya, wadda ta samu ’yancin-kai a 1964, kuma ta yi
shugabanni bakwai da kuma shugaban kasa na rikon-kwarya guda daya. Shugaban
kasar na yanzu shi ne Hakainde Hichilema.

Dukkan shugabannin da suka gabace shi sun rasu, ciki har da guda biyu da suka
rasu a cikin shekarar da ta gabata. Edgar Lungu ya rasu a watan Yunin 2025, yayin
da tsohon shugaban kasa na rikon kwarya Guy Scott ya rasu a ranar 15 ga Yuli,
2026.

Bari mu koma kasar Uganda, wadda ta samu ’yancin-kai a shekarar 1962.
Shugabanta a yau, Yoweri Museveni yana kan mulki tun shekarar 1986, kuma duk
wani shugaba da ya mulki kasar kafin shi, tun daga kan Milton Obote zuwa kan Idi
Amin, duk ba sa duniya.

Ita kuwa Jamhuriyar Congo, wadda aka fi sani da Congo-Brazzaville, ta yi
shugabanni da dama tun bayan samun ’yancin-kanta a shekarar 1960.
Shugaba mai ci yanzu, Denis Sassou Nguesso, ya dawo mulki a shekarar 1997
bayan ya taba yin mulki daga shekarar 1979 zuwa 1992.

Ita ma Congo-Brazzaville duka sauran tsofaffin shugabanninta sun rasu.
A kasar Togo kuwa, akwai Shugaba Faure Gnassingbé wanda ya gaji mulki daga
hannun mahaifinsa Gnassingbé Eyadéma, wanda ya rasu a shekarar 2005.

Kasar ta yi shugabanni da dama tun bayan samun ’yancin-kai a shekarar 1960,
amma a yau ba ta da ko da tsohon shugaban kasa guda daya da yake raye a yanzu.
Ita ma kasar Djibouti wadda ta samu ’yancin-kai tun a 1977, a yau bayan shekaru
49, shugabanni biyu kacal suka taba jagorantar ta.

Ismaïl Omar Guelleh, shi ne shugaban Djibouti a yanzu kuma ya hau mulki ne tun
a 1999. Wanda ya gabace shi, Hassan Gouled ya rasu a shekarar 2006.

Idan muka dubi kasar Eswatini, masarauta ce da ta samu ’yancin-kai a shekarar
1968, kuma ba ta da tsarin shugaban kasa.

Sarki Mswati III ne ke kan mulki tun 1986, kuma babu wasu tsofaffin sarakuna da
suka jagoranci kasar da ke raye a yanzu.

Sarkin shi ne shugaban kasa, yayin da yake da firaiminista, wanda a halin yanzu shi
ne Russell Mmiso Dlamini, a matsayin shugaban gwamnati.

Batun kasancewar tsofaffin shugabannin kasa a raye yana da nasa alheran da
kuma matsaloli.

Masana harkokin siyasa sun bayyana cewa tsofaffin shugabanni
za su iya amfanar da kasarsu da shawarwari da hikima da taimaka wajen kulla
kyakkyawar dangantaka da kasashen ketare.

Kazalika za su iya ba kasarsu muhimman shawarwari lokacin da kasashen suke cikin mawuyacin hali saboda gogewar da suke da ita.

Sai dai akwai wasu da suke ganin tsofaffin suna taka rawa wajen raba kan
al’umma, lakume makudan kudin kasa saboda hidimar da ake musu da kuma
zama tarnaki ga sababbin shugabanni masu kokarin samar da tasu hanyar ta ci
gaba.