| Hausa
GABAS TA TSAKIYA
2 minti karatu
Ubangiji ba ya karɓar addu'ar waɗanda suke ƙaddamar da yaƙi - Fafaroma
Fafaroma Leo XIV ya yi gargadi ranar Lahadi cewa, Allah "ba ya karɓar addu'ar wadanda suke ƙaddamar da yaƙi" yayin da yaƙi ke ci gaba da ta'azzara Gabas Ta Tsakiya.
Ubangiji ba ya karɓar addu'ar waɗanda suke ƙaddamar da yaƙi - Fafaroma
Ubangiji ba ya karɓar addu'ar waɗanda suke ƙaddamar da yaƙi - Fafaroma / Reuters

Fafaroma Leo XIV ya yi gargadi a ranar Lahadi cewa Allah "ba ya sauraron addu'ar waɗanda suke ƙaddamar da yaƙi" yayin da rikici a Gabas ta Tsakiya ke ci gaba da ta’azzara a ɓangarori da dama.

“Haka Ubangijinmu yake... Ubangiji wanda ba ya son yaki... wanda ba ya sauraron addu'ar waɗanda ke yin yaƙi,” ya faɗa a yayin wa'azin da ya gabatar a ranar Lahadi, na Palm Sunday.

Bayan addu'ar Angelus, ya yi ta'aziyya ga waɗanda rikici ya shafa a Gabas ta Tsakiya, "wadanda ke shan wahalar sakamakon mummunan rikici kuma a lokuta da dama ba za su iya gudanar da cikakkiyar ibada na waɗannan ranakun masu tsarki ba."

A farkon wannan makon, Fafaroma ya yi kira ga tsagaita wuta a rikicin Gabas ta Tsakiya, yana cewa an tilasta wa fiye da mutum miliyan ɗaya barin gidajensu kuma ya roƙi ɓangarorin da ke yaki su zauna su sasanta.

Ya yi kira da a yi sulhu

Leo XIV, fafaroma na farko daga Amurka, ya sha yin Allah wadai da yaƙi kuma ya yi kira ga tattaunawa.

Amma fafaroman mai shekaru 70 ya kasance mai taka tsantsan a cikin bayanansa tun bayan harin da Amurka da Isra'ila suka kai kan Iran wanda ya ƙaddamar da yaki a 28 ga Fabrairu, inda ya nisanci ambaton sunan kowane ɓangare a cikin Allah wadai da roƙonnin zaman lafiya da yake yawan yi.

Rumbun Labarai
Mene ne Tehran ke gabatarwa domin kawo ƙarshen yaƙin Amurka da Isra'ila a kan Iran?
Araghchi ya faɗaɗa zirga-zirgar diflomasiyyar Iran daga Islamabad zuwa Moscow
Sisi na Masar ya yi gargaɗi kan 'ƙoƙarin da ake yi da gangan' na sake zana taswirar Gabas ta Tsakiya
Falasɗinawa na kaɗa ƙuri'a a zaɓen farko tun bayan yaƙin ƙare-dangi da Isra'ila ta ƙaddamar a Gaza
Iran ta ce ba kai-tsaye za a yi tattaunawa a Pakistan don kawo ƙarshen yaƙin Amurka da Isra’ila ba
Turkiyya da ƙasashe bakwai sun soki Isra'ila kan keta alfarmar Masallacin Ƙudus
Trump ya fasa kai wa Iran hari da makamin nukiliya
Daraktan IEA ya ce ana asarar gangar mai miliyan 13 kullum saboda rufe Mashigar Hormuz
Amurka ta dakatar da jigilar dala zuwa Iraƙi, amma me ya sa take aika kuɗi zuwa Baghdad?
Trump ya tsawaita tsagaita wutar Iran domin bai wa Tehran ƙarin lokaci na tattaunawa
Vance zai tafi Pakistan ranar Talata domin tattaunawa da Iran  — rahoto
Sojan Isra’ila na shan suka bayan ya lalata mutum-mutumin Yesu a Lebanon
Iran ta kai harin ramuwar gayya kan jiragen Amurka a kan ƙwace jirgin dako: Rahoto
Isra'ilawa da dama sun mamaye Masallacin Ƙudus a ƙarƙashin rakiya da tsaron 'yansanda mai tsanani
Trump ya ce Amurka na yin tattaunawa mai kyau da Iran, ya yi gargaɗi kan rufe Mashigar Hormuz
Hare-haren Iran sun lalata fiye da gidaje 1,000 tare da mayar da su kufai a Tel Aviv - Magajin Gari
Iran ta kama mutum 127 kan zargin taya abokan gaba shirya kai mata hari ta ƙasa
Trump ya ce za a yi amfani da ‘manyan katafilolin tone kasa’ don kwashe sinadarin Uranium daga Iran
Iran ta sanar da bude Mashigar Ruwa ta Hormuz ga dukkan jiragen ruwan duniya
Jakadan Iran a MDD ya bayyana ƙawanyar Amurka a matsayin 'matakin tsangwama'