‘Yan ƙasashen waje aƙalla 18 na cikin mutum 21 da wata gobarar otel ta kashe a babban birnin Indiya Delhi ranar Laraba, kamar yadda kafafan watsa labaran ƙasar suka ruwaito.
Waɗanda suka mutu sun haɗa da ‘yan ƙasashen Nijeriya da Mozambique da Laberiya, kamar yadda rahotannin suka ruwaito.
Ma’aikatar harkokin wajen Indiya tana magana da ofisoshin jakadancin ƙasashen da lamarin ya shafa kuma tana bayar da taimakon da ake buƙata, kamar yadda Ministan Harkokin Wajen Indiya Subrahmanyam Jaishankar ya bayyana a wani saƙon da ya wallafa a shafin X.
Rundunar ‘yansandan Indiya ta kama mai otel din yayin da masu bincike ke nazari kan gazawar matakan kariya. Rundunar ‘yansandan ta ce an kama mai otel ɗin Lavkesh Bajaj da yammacin ranar Laraba , sa’o’i bayan gobarar ta ci ginin.
Ana yawan samun gobara a gidaje a Indiya saboda rashin kayayyakin kashe gobara da kuma yin biris da dokokin kariya.
Mafi shahara ga mara lafiya
Gobarar - mafi muni da ƙasar ta gani tun shekarar 2022 - ta ɓarke ne a wani otel a unguwar Malviya Nagar ta Delhi, wadda kafafan watsa labarai suka ce ta shahara wajen zaman mara lafiya da iyalan waɗanda ake yi wa magani a wani asibitin da ke kusa .
Za a kai samame kan dukkan masauƙin baƙi a faɗin birnin da sauran wurare da ke saɓa dokokin kariya da dokokin gine-gine, in ji ofishin babbn ministan birnin a saƙon da ya wallafa a shafin X da yammacin ranar Laraba .
Za a rufe wuraren da ba su yi biyayya ga dokokin ba za a kuma gurfanar da waɗanda suka aikata hakan, in ji sanarwar.








![Masar ta yi kira ga kwamitin tsaro na MƊD ta dakatar da faɗaɗa [harin] da Isra'ila ke yi a Lebanon](https://d2udx5iz3h7s4h.cloudfront.net/2026/4/25/67480fcc1bc16e3971fbb70d/image/35fa6aac64e41c9240c09651b2ba0fb1be4eb5b1e1ca009d1c3d191c8f65622b.webp?width=512&format=webp&quality=80)





