| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
Masarautar Kano ta musanta bidiyon da ake yadawa kan Sarki Sanusi II ya samu 'carry-over' a jami'a
Bidiyon, wanda ya bazu sosai a shafukan sada zmunta a ranar Lahadi, ya yi zargin cewa tsohon Gwamnan Babban Bankin Nijeriya bai cika ƙa’idar cin nasarar ɗaya daga cikin darussansa ba.
Masarautar Kano ta musanta bidiyon da ake yadawa kan Sarki Sanusi II ya samu 'carry-over' a jami'a
A halin yanzu, Sarki Sanusi ɗalibi ne a mataki a ji biyu na sashen digirin shari’a a jami’ar.

Masarautar Kano da ke arewacin Nijeriya ta yi watsi da wani bidiyo da ya yaɗu a kafafen sada zumunta, wanda ke iƙirarin cewa Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na II, ya samu kari-oba a ɗaya daga cikin darussan Shari’a da yake karatun digiri a kai a Jami’ar Northwest da ke Kano, kamar yadda kafofin watsa labaran ƙasar suka ruwaito.

Bidiyon, wanda ya bazu sosai a ranar Lahadi, ya yi zargin cewa tsohon Gwamnan Babban Bankin Nijeriyar bai cika ƙa’idar cin nasarar ɗaya daga cikin darussansa ba.

A halin yanzu, Sarki Sanusi ɗalibi ne a mataki a ji biyu na sashen digirin shari’a a jami’ar.

Sai dai Sakataren Ofishin Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammad Ado, ya bayyana cewa zargin ba gaskiya ba ne, yana mai cewa Sarkin na ci gaba da tafiyar da karatunsa yadda ya kamata da burin kammala jami’ar da digiri mafi daraja (First Class).

A cewarsa, bayanan da Masarautar ke da su sun nuna cewa Sarkin na buƙatar maki ɗaya kacal domin cim ma matakin maki mafi daraja, kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.

Masu AlakaTRT Afrika - Tarihin Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II

“Mun halarci wani shiri da ɗaliban shari’a suka shirya a jami’ar a ranar Asabar, kuma wani ɗalibi ne ya ɗauki bidiyon. Amma abin da ake yaɗawa ba gaskiya ba ne.

“A lissafinmu, maki ɗaya ne kawai ya rage wa Mai Martaba domin ya samu First Class. Sunday Dare ne ya halarci shirin a matsayin baƙon malami,” in ji Ado.

Shi ma wani ɗalibin jami’ar, Ibrahim Abubakar-Danmasani, ya musanta wannan iƙirari, yana mai cewa har zuwa ranar Lahadi ba a fara jarrabawar jami’ar ba.

Ya ce an tsara fara jarrabawar ne a ranar Litinin.

Majiyoyi daga cikin jami’ar su ma sun tabbatar da bayanin Masarautar, suna cewa bidiyon da ya yaɗu ba ya nuna ainihin matsayin karatun Sarkin Kano.

Sun ƙara da cewa wasu matasa ne suka ɗauki tare da yaɗa bidiyon a matsayin wasa, abin da daga baya ya rikide ya zama jita-jita a kafafen sada zumunta.

 

 

Rumbun Labarai
Nijeriya da Amurka sun ƙulla yarjejeniyar biliyan $700 a ɓangaren haƙar ma'adinai
Ƙungiyar Amnesty International ta soki gwamnatin jihar Kano a Nijeriya kan musguna wa ‘yan adawa
Ba na da-na-sanin taimaka wa waɗanda suka yi watsi da ni a yanzu— El-Rufai
Tsaro a Arewa maso Yammacin Nijeriya: Me ke bayan raguwar kashe-kashe, me ke ƙara tayar da hankali?
Kalaman Malami da Fagbemi sun ci karo da juna kan yarjejeniyar sulhu ta $200m kan aikin Mambila
Gwamnatin Nijeriya ta bayar da wa’adin mako biyu don bincike kan mutuwar mutum 37 a hannun NSCDC
Ana zargin wasu ’yan siyasar Nijeriya da karkatar da $271m na gwamnati sun sayi gidaje a Amurka
An gudanar da zanga-zangar neman a kubutar da daruruwan mutane da aka yi garkuwa da su a jihar Neja
Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta ce Shettima na da cikakken ikon wakiltar Tinubu a taron UNGA
Matsalar haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba a Nijeriya
'Yanbindiga sun kashe mutum tara a jihar Filaton Nijeriya
An kama mai PoS da ake zargi da aiki da taimakon mai garkuwa da mutane
An tsare kwamandan NSCDC da wasu jami'an hukumar na jihar Neja kan mutuwar masu haƙar ma'adinai 37
Gwamnatin Nijeriya ta kafa kwamitin mutum 10 don binciken mutuwar mutum 37 a hannun NSCDC a Neja
Waɗanda suka tsira a Jihar Neja sun bayyana yadda abokan sana'arsu suka rasu a ɗakin da aka tsare su
Ana zargin giya ta kashe mutum 49 a Jihar Ondo da ke kudancin Nijeriya
Gwamnatin Nijeriya ta dakatar da kwamandan NSCDC bisa mutuwar masu haƙar ma'adinai 37 a jihar Neja
Majalisar Wakilan Nijeriya ta aika da ƙudirin kafa ’yansandan jihohi ga majalisun dokokin jihohi
Rikicin Amurka da Iran: NLC ta nemi gwamnatin Nijeriya ta ɗauki mataki bayan litar mai ta kai N1,500
Dakarun Nijeriya sun kubutar da mutane 31 da aka yi garkuwa da su a jihohin Katsina da Kebbi