| Hausa
WASANNI
3 minti karatu
Iran za ta buga wasannin Gasar Kwallon Kafa ta Duniya a Amurka duk da rikici, in ji FIFA
Tabbacin na zuwa ne makonni bayan jita-jita, inda shingen diflomasiyya da batutuwan kan iyaka ke rikita shirye-shiryen da ake yi.
Iran za ta buga wasannin Gasar Kwallon Kafa ta Duniya a Amurka duk da rikici, in ji FIFA
Kwallon kafar gasar kofin duniya a wani shago a birnin tehran na Iran, a ranarl 23, ga Afrilun 2026. / Reuters Archive

Shugaban FIFA Gianni Infantino ya sake nanata cewa Iran za ta buga wasanninta na gasar cin kofin duniya a Amurka kamar yadda aka tsara, yayin da ya kaddamar da fara taron hukumar kwallon kafa ta duniya a Vancouver.

Shiga Iran a gasar wannan shekarar a Canada, Mexico da Amurka ya kasance cikin rashin tabbas tun bayan barkewar yaki a Gabas ta Tsakiya a watan Fabrairu bayan hare-haren da Amurka da Isra'ila suka kai.

Infantino, wanda ya sha nanata cewa Iran za ta halarci gasar cin kofin duniya, ya jaddada wannan matsayin a farkon jawabinsa ga wakilai a Vancouver.

"Bari in fara da farko, ina tabbatar da cewa ba shakka Iran za ta shiga gasar cin kofin duniya ta FIFA ta 2026," in ji Infantino a ranar Alhamis. "Kuma ba shakka, Iran za ta buga a Amurka."

Jami'an Iran sun yi ta yada ra'ayin sauya wasannin rukuni daga Amurka zuwa Mexico, amma Infantino ya riga ya yi watsi da wannan shawarar.

A wani sabon salo a makon da ya gabata, an rawaito cewa wakilin musamman na Amurka Paolo Zampolli wanda aka haifa a Italiya ya yi watsi da ra'ayin Italia na kwace gurbin gasar cin kofin duniya ta Iran.

Daga baya gwamnatin Amurka ta nisanta kanta daga wannan shawara, inda Sakataren Harkokin Wajen Amurka Marco Rubio ya ce za a marabci 'yan wasan kwallon kafa na Iran.

Amma tashin hankalin da ke tattare da halartar Iran gasar cin kofin duniya ya kara ta'azzara har zuwa taron FIFA na ranar Alhamis.

Iran ce kadai wadda ba ta halarci taron majalisar mai mambobi 211 ba yayin da taron ranar Alhamis ya fara bayan wani rikici da jami'an kan iyaka na Canada a farkon wannan makon.

Jami'an hukumar kwallon kafa ta Iran (FFIRI) sun bar Canada ba zato ba tsammani bayan sun sauka a Toronto, inda suka kuma yi watsi da tafiyarsu ta gaba zuwa Vancouver.

Kafafen yada labarai na Iran sun ce shugaban FFIRI Mehdi Taj - tsohon mamba na rundunar kare juyin juya halin Musulunci ta Tehran (IRGC) - da abokan aikinsa biyu sun tashi zuwa gida bayan da jami'an shige da fice na Canada suka "zage" su.

Canada, wacce ta ayyana IRGC a matsayin kungiyar ta'addanci a shekarar 2024, ta fada a ranar Laraba cewa mutanen da ke da alaƙa da rundunar "ba za a yarda da su ba."

"Duk da cewa ba za mu iya yin tsokaci kan al’amuran daidaikun mutane ba saboda dokokin sirranta bayanau, gwamnati ta bayyana karara kuma ta yi daidai: jami'an IRGC ba za su iya shiga Canada ba kuma ba su da matsayi a ƙasarmu," in ji hukumar shige da fice ta Canada a cikin wata sanarwa.

Iran, wacce za ta zauna a Tucson, Arizona a lokacin gasar cin kofin duniya, za ta fafata da New Zealand, Belgium da Masar a rukunin G.

'Yan Iran za su bude gasar cin kofin duniya da New Zealand a Los Angeles a ranar 15 ga Yuni.