Shugaban Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana a ranar Jumma’a cewa ya kamata a kawo ƙarshen yaƙi da Amurka yayin da Iran ke da matsayin “iko da mutunci,” inda da ya kare yarjejeniyar da Tehran ta ƙulla ranar 18 ga watan Yuni da Amurka.
Da yake magana a wani taro, Pezeshkian ya ce sakamakon tattaunawar ya kasance “muhimmiyar nasara” da Majalisar Tsaro ta Ƙolin Iran ta amince da ita, in ji wata sanarwa daga fadar shugaban ƙasar Iran.
“Abin da aka cim ma yayin tattaunawar wata muhimmiyar nasara ce,” a cewarsa, yana mai ƙarawa da cewa mambobin majalisar waɗanda ke da hannu a ciki sun kare shi sosai.
Pezeshkian ya bayyana yarjejeniyar da aka ƙulla kwanan nan a matsayin abu na “mutunci da ƙima,” yana mai watsi da sukar cewa Tehran ta sarayar da wasu abubuwa.
“Ba za su iya samun ko sashe ɗaya a cikin wannan yarjejeniyar da ke nuna miƙa wuya ba; dukkan alƙawuran suna da alaƙa ne da ɗaya ɓangaren,” in ji shi.
Sai dai shugaban Iran ya jaddada cewa yarjejeniyar ba ta nufin Tehran za ta miƙa wuya idan aka kai wani hari.
“A ko wane yanayi ba za mu miƙa wuya ga cin zarafi ba,” in ji shi. “Za mu tsaya tsayin daka a har iya ƙarshen numfashinmu kuma za mu ba su martani mai ƙarfi.”
Pezeshkian ya ce ya kamata a ce yaƙin ya kawo ƙarshe a wani lokaci, yana mai cewa yanayi da ake ciki yanzu ya ba da damar da ta dace.
“Ya kamata a kawo ƙarshen yaƙin a yau, a lokacin da muke da cikin wani matsayi na iko da mutunci,” in ji shi, yana mai cewa Amurka ta keta dokokin ƙasa da ƙasa ta hare-haren da ta kai wa makarantu da asibitoci da ababen more rayuwa a Iran.
Ya ce kwamandojin soji da dakarun Iran suna shirye domin kare ƙasar, yayin da yake jaddada muhimmancin ci gaba da haɗin kai a cikin ƙasar.
Iran da Amurka sun rattaba hannu kan wata yarjejeniya mai sharruɗa 14 a ranar 18 ga watan Yuni bisa shiga tsakani na Pakistan da Qatar, lamarin da ya ba da damar kawo ƙarshen yaƙin da kuma kwanaki 60 na tattaunawa domin cim ma yarjejeniya ta ƙarshe.
Daga baya Tehran ta zargi Washington da saɓa sharuɗɗan tattaunawar, yayin da Pakistan da Qatar suka ci gaba da shiga tsakanin ɓangarorin biyu.

















