Mataki na gaba na tattalin arzikin intanet na Afirka zai iya samuwa ne bisa abin da nahiyar za ta samar maimakon abin da ta rasa.
Wannan shi ne ra’ayin Adeniyi Adebayo, Babban Jami’in Kasuwanci a kamfanin neman motocin hawa ta Yango Ride, wanda ya ce rashin manyan ababen more rayuwa ya bai wa da yawa daga cikin ƙasashen Afirka wata dama wadda ba kasafai aka fi samu ba ta tsallakaewa zuwa zamanin Ƙirƙirarriyar Basira da sarrafa bayanai ta intanet da kuma kafafan intanet.
Da yake magana da TRT Afrika, Adebayo ya ce nahiyar tana shiga wani zamani inda fasahar za ta iya sauya ba wai ayyuka da ake ta intanet kawai ba, har ma da noma da sufuri da ƙera abubuwa da kuma samar da ababen more rayuwa.
Bankin Duniya ya yi ƙiyasin cewa tattalin arziki na intanet yana ba da gudumuwar kashi 5 cikin 100 ga kimar tattalin arzikin Afirka a ma’aunin GDP, kuma masu sharhi suna tsammanin kason zai iya ƙaruwa bisa yadda damar amfani da intanet ta waya ƙe faɗaɗa tare da ƙara kasancewa jiki a rayuwar yau da kullum.
“Idan ka ka kwatanta Asiya da Afirka da Turai da Kuma Arewacin Amurka, za ka ga cewa muna da tattalin arziki na intanet da ya fi girma a duniya .”
Waɗanda suka ga yadda tatalin arziki na intanet ya shigo
Ga Adebayo, matakin sauyin zai bayyana idan aka kalle shi ta hanyar tunanin mutum maimakon ƙididdiga.
“A cikin shekaru ashirin da biyar da suka gabata, babu wani abu mai kama da tattalin arziki na intanet a faɗin duniya, musamman ma a Afirka. Na tuna sosai lokacin da mahaifiyata ta sayi waya samfurin Nokia 3310 a shekarar 2002.”
Wannan lamarin, in ji shi, ya nuna yadda wata masana’anta za ta iya bayyana da kuma samar da kima mai yawa.
“Masana’antar gaba ɗaya ba ta wuce shekara 25 ba. Kamfanoni irin su Alphabet da Microsoft kimarsu ta kai tiriliyoyin daloli. Idan kai ɗankasuwa ne, abu ne mai kyau mutum ya shiga cikin wani kasuwanci da ke girma cikin sauri kamar haka.”
Abin da ya sa Afirka za ta iya wuce sauran yankuna wajen amfani da fasahar
Adebayo ya yi imanin cewa ɗaya daga cikin abin da Afirka ta fi saura da shi shi ne fannoni da yawa ba sa ɗauke da nauyin tsarin baya.
“Ga da dama daga cikin ƙasashen Afirka, ba mu da fasahohi da yawa na da ko kuma kasuwanci na da. Wannan na nufin za mu iya ƙara abu cikin sauri da koyon amfani da sabbin fasahohi da tsare-tsare cikin sauri.”
Ya yi ishara ga fannin sadarwa a matsayin mafi bayyanar kwatance. Kafin wayoyin salula su iso, faɗaɗa wayar tarho na buƙatar kayayyaki na waya masu tsada. Fasahar wayar salula ta bai wa ƙasashe damar iya haɗa miliyoyin mutane ba tare da gina wata cibiya mai faɗi ba.
“Kana da dama a Afirka ta iya tsallakewa zuwa waɗansu daga cikin waɗannan matakan da kuma gini kai-tsaye zuwa wannan matakin.”
Misali na Rwanda: tsallake hanyar da ba nan
Domin bayyana abin da tsallakewa ke nufi a aikace, Adebayo ya ba da misali da Zipline, kamfanin aika ta jirage mara matuƙa da aka samar a Rwanda.
“Sun yi jirage mara matuƙi domin aikewa da magunguna zuwa wurare masu nisa. Me yasa kake buƙatar jirage mara matuƙa? Saboda babu hanyoyi. Za ka iya tsallake maganar cewa ba ka da hanyoyi kuma ka iya kai magunguna.”
Daga gare shi, wannan wani babban darasi ne na Afirka: samar da sabon abu ba ko da yaushe ne yake buƙatar sake hanyar samar da ababen more rayuwa da Turai da Arewacin Amurka suka bi ba.
Adebayo ya ce ƙirƙirarriyar basira tana sauya ilimi na halin yanzu, amma yana tsakanin matakinsa na gaba ya shigo cikin duniya ta butunbutumi da jirage mara matuƙa da kuma tsare-tsare masu sarrafa kansu.
“A yau AI na sauya hanyoyin yadda wurare na intanet da kuma aikin ilimi ke faruwa. Daga baya zai fantsama zuwa cikin duniya ta zahiri.”
Ya ce wannan zai iya rage tsadar yadda ake samar da abubuwa a fannoni daban daban.
“Ka raya zuciyarka wani zamani inda wani butunbutumi na AI zai iya yin abubuwa na ƙwarewa da ke sa ayyuka na samar da ababen more rayuwa ke tsada. Ilimi zai kasance wani abu da aka rarraba, kuma tsadar amfani da wannan ilimin zai faɗi sosai.”
A nashi ra’ayin, lamarin ya zarce kamfanonin fasaha.
“Nan gaba zai kasance abu mai ban sha’awa saboda AI zai iya kawo juyin juya hali ga noma da abinci da sufuri da masana’antu da fannoni da yawa. Abin da muke gani a halin yanzu farko ne kawai.”
AfCFTA: Tsarin siyasa, buƙata ta tattalin arziki
Adebayo yana ganin yarjejeniyar kasuwanci babu shamaki a Afirka a matsayin wani muhimmin ɓangare na makomar intanet a nahiyar, duk da cewa ya amince da matakin ƙalubalen.
“Muna da fiye da mutum biliyan ɗaya da suke rabe a cikin ƙasashe 54. Abin da gwamnatoci suke ƙoƙarin yi ba shi da sauƙi.”
Ya ce Tsarin biyan kuɗi na Afirka (PAPSS), wanda ke tallafa wa tsarin biyan kuɗi daga wata ƙasa zuwa wata ƙasa cikin kuɗaɗe na ƙasashen, wani muhimmin mataki ne na farko.
“Yanzu kuɗi zai iya tafiya cikin sauƙi fiye da da. Wannan wata tafiya ce mai kyau a hanyar da ta dace.”
Amma ya ce biyan kuɗi kawai bai isa ba.
“A gaba muna buƙatar tafiyar kayayyaki da ayyuka da kuma mutane. Idan muka sami waɗannan matakai na gaban, ina ganin wani zamani na wadata mai yawa na jiran Afirka.”
Kasuwanci daga farko, sannan ababen more rayuwa
Ɗaya daga cikin dalilan Adebayo da suka fivsauri shi ne gwamnatocin Afirka su mayar da hankali kan tallafa wa kasuwanci kafin tsarin yanzu ya warware komai.
“A lokacin da kake da kasuwanci, sannan kana da wani abin da za ka ɗaura wa haraji. Idan babu kasuwanci, babu abin da za ta ɗaura wa haraji.”
Ya kwatanta tattalin arzikin ƙasashe da suka fi dogara ga haƙo ma’adinai da waɗanda suke samu kuɗaɗen shiga ta hanyar cinikayya tsakanin kamfanoni da masu sayan kayayyaki.
“A yau gwamnatocin Afirka da yawa suna saka haraji kan abubuwan da suka fito daga ƙasa, ba abubuwan da suka faru a tsakanin mutane ba. Idan za ka iya saka haraji kan cinikayya tsakanin mutane, za ka iya samar da ginshiƙi na kuɗi domin zuba jari kan ababen more tayuwa.”
Adebayo ya ce nahiyar tana riga ta samu ƙwarya-ƙwaryar haɗin kai a fannin sadarwa kuma a wasu yankuna a fannin kaikomon mutane.
“Ba na biyan ko wane haraji kafin na yi magana da kai. Muna da WhatsApp da Zoom da sauran manhajoji. Akwai kaikomon sadarwa ba tare da tsaiko ba.”
Ƙungiyoyin ƙasashe na yankuna irin su ECOWAS da ƙungiyar raya tattalin arzikin ƙasashen Gabashin Afirka sun samu ci-gaba a fannin tafiya.
“Abin da ba mu buɗe gabaɗaya ba shi ne kaikomin kudi da kayayyaki cikin sauƙi.”
Tsaikon ƙa’idoji
Ga kamfanonin da suke aiki a faɗin kasuwannin Afirka, saka ƙa’idoji a rarrabe ya kasance babban ƙalubale.
“Idan kana yi wa Yango tuƙi a Côte d’Ivoire, akwai wani jerin dokoki ga motoci da matuƙa da kuma abokan aiki na tasi. Waɗannan dokokin ba sa aiki kai tsaye a Kamaru ko Senegal.”
Ko wace sabuwar kasuwa tana buƙatar sabbin yarjejeniyoyi da kuma hanyoyin biyayya ga dokoki.
“Idan ka je sabuwar ƙasa, kuma sabuwar magana ce da jerin sabbin dokoki.”
Adebayo ya ce salon aiki Yango shi ne ta tattauna a fili da masu saka ido da gwamnatoci, da faɗaɗɗiyar burin samar da tsare-tsare da ke tallafa wa hidindimu da suke ƙetare kan iyakoki.
Duk da jerin ƙalubalen, Adebayo ya kasance mai burin cewa ƙarin hadin kai zai iya buɗe ƙarin matakai na cinikayya tsakanin ƙasashen Afirka masu maƙwabtaka.
“Idan muka kawo ababen more rayuwa da suka dace da kuma dokokin da suka dace, babu wani dalilin da zai sa babu ƙarin cinikayya tsakanin ƙasashe maƙwabta fiye da yadda muke da shi ba a yau.”
A gare shi, babban labarin ba wai kawai girman manhajojin neman motoci ba ne kawai. Shi ne yiwuwar Afirka za ta iya haɗa fara amfani da intanet da wuri da fara amfani da AI da kuma kasuwar nahiya mai ƙarin haɗin kai ta samar da wani sabon matakin ci-gaba na tattalin arziki.
“Muna farko-farko ne kawai. Damar ba kawai ta mayar da kasuwanci ta intanet ba ce kawai, amma ta samar da sabbin tsare-tsare da a da ba za su yiwu ba.”





















