Dakarun sojin saman Sudan sun daƙile hare-haren wasu jiragen sama marasa matuƙa da ake zargin rundunar RSF ce ta ƙaddamar da su a wani yunƙuri na kai hari kan yankunan fararen-hula a jihohin Khartoum da River Nile, a cewar rahoton kamfanin dillacin labarai na Sudan News a ranar Laraba.
Rahoton ya ce tsarin tsaron sararin samaniya na rundunar sojin Sudan ya yi luguden wuta kan jiragen, yayin da aka ruwaito cewa an gano wasu jiragen sama marasa matuƙa a birnin El-Obeid da ke jihar North Kordofan.
Kawo yanzu dai ba a fitar da wani ƙarin bayani ba game da yawan asarar rai ko barnar da aka samu ba, sannan RSF ba ta yi tsokaci kan hare-haren da aka ruwaito ba.
Hare-haren sun biyo bayan abin da kafar Sudan News ta ce koma-bayan da RSF ta fuskanta a fannoni da dama a yankin Kordofan, inda sojojin Sudan suka kara kaimi a ayyukan soji kwanan nan.
Kwace muhimman wurare
Kafar yada labaran ta ce hare-haren sun kuduri aniyyar kara wa dakarun RSF kwarin gwiwa bayan asarar da suka yi a fagen daga, ko da yake ba a iya tabbatar da wannan ikirari na kafar ba.
Kazalika, rahotannin hare-haren RSF sun zo ne a daidai lokacin da sojojin Sudan suka fadada ayyukansu a yankin Kordofan, inda suka ce sun kwace jerin garuruwa da wurare masu mahimmanci daga hannun RSF a 'yan makonnin nan bayan sun ƙara ƙaimi wajen karbe iko kan Khartoum a farkon wannan shekarar.
Rundunar RSF tana ƙara amfani da jiragen sama marasa matuƙa masu cin dogon zango don kai hari kan wuraren sojoji da muhimman kayayyakin more rayuwa a yankunan da sojojin Sudan ke iko da su, inda hare-haren baya-bayan nan suka afka kan Port Sudan da Atbara da Dongola da sauran biranen da ke nesa da manyan wuraren yaƙi.
Tun a watan Afrilun 2023 Sudan ta tsuduma yaƙi, bayan fada ya barke tsakanin sojojin Sudan da dakarun RSF kan shirin hada rundunar da na Sojojin Sudan wuri guda.
Yakin ya yi sanadiyar kashe dubban mutane, tare da raba miliyoyi da muhallinsu, sannan ya haifar da daya daga cikin matsalolin jinƙai mafi muni a duniya.






















