Kansar gaban tsohon Shugaban Amurka Joe Biden ta yaɗu zuwa wasu sassan jikinsa kuma tana haddasa raɗaɗi mai yawa, in ji ɗansa, Hunter Biden, wanda ya tattauna halin da tsohon shugaban ƙasar ke ciki a wata hira.
Yayin wata doguwar hira da BBC ranar Jumma’a, Hunter Biden ya kasance wanda ke cikin wani hali na sosa rai yayin da yake magana game da lafiyar mahaifinsa, yana mai cewa abu mai wuya ne kallon yadda yake.
"Kansar ta yaɗu, ta yaɗu zuwa cikin ƙasusuwansa da ma fiye da nan," in ji shi. "Abu ne mai raɗaɗi sosai, kuma yana kasarrawa ta hanyoyi daban daban."
Hunter Biden ya ce gano cewa yana da cutar abu ne mai wahala ga iyalinsa.
"Kallonsa abu ne na baƙin ciki," in ji Biden. "Abu ɗaya da zan ni iya faɗa game da mahaifina, game da lafiyarsa a halin yanzu, shi ne na so ya kasance zai ƙara yawan ƙorafi, saboda abu ne mara kyau."
Suka game da lafiyar Biden
A matsayinsa na mai shekara 83, Biden ya kasance mutum mai mafi yawan shekaru da ya taɓa riƙe ragamar mulkin Amurka, inda yawan shekarunsa ya zama abin da aka fi damuwa da shi cikin shekaru huɗu da ya yi a ƙaragar mulki.
Biden da masu ba shi shawara a fadar White House sun kasance ƙarƙashin wata babbar suka bisa zargin cewa sun ɓoye tsananin matsalolin lafiyarsa, musamman bayan ya gama gangamin yaƙin zaben neman komawa wa’adi na biyu na mulkin biyo bayan muhawara mai muni da ya yi da wanda ya gaje shi dagabaya, Donald Trump.
Biyo bayan wata muhawara mai muni da Trump a watan Yunin shekarar 2024 da kuma matsi daga ‘yan jam’iyyar Democrats, Biden ya janye daga zaɓen shugaban ƙasar.
Trump ya samu ya yi nasara kan wadda ta maye gurbin Biden — mataimakiyar shugaban ƙasar ta wancan lokacin Kamala Harris.
Tsohon Shugaban ƙasar ya bayyana cewa yana da cutar kansa ne a watan Mayun shekarar da ta gabata, ƙasa da watanni huɗu bayan ya bar fadar White House.





















