| Hausa
GABAS TA TSAKIYA
3 minti karatu
Hantarar da Amurka ke yi mana za ta ta'azzara ƙoƙarin diflomasiyya, in ji Iran
Jami'an Iran sun ce Tehran tana da wani "tsarin shiri na shekaru biyu" don jure wa sabbin takunkuman Washington, suna masu bayyana cewa Amurka ta sha ƙokarin karya logon mutanen Iran a lokuta da dama.
Hantarar da Amurka ke yi mana za ta ta'azzara ƙoƙarin diflomasiyya, in ji Iran
Shugaban Iran Masoud Pezeshkian ya ce zaluncin Amurka zai rikidar da tsarin zaman lafiya

Shugaban Iran Masoud Pezeshkian ya ce dole ne Amurka ta sauya salonta ta mu’amala da Tehran, yana mai gargaɗin cewa mayar da hankali kan hantara da "zalunci" zai ta'azzara ƙoƙarin diflomasiyya.

"Dole ne Amurka ta gyara salonta da tsarinta wajen mu'amala da Iran, domin dogaro kan hantara da zalunci za su ta'azzara tsarin aiwatarwar da yarjejeniyar fahimtar juna tsakanin Iran da Amurka da Pakistan ta jagoranta ne kawai,” a cewar Pezeshkian a yayin ganawarsa da Babban Jami'in Sojan Pakistan Asim Munir a Tehran ranar Litinin.

Pezeshkian ya bayyana cewa samar da zaman lafiya da tsaro mai ɗorewa a yankin tare da haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen Musulmai shi ne abin da ake "matukar buƙata."

A halin da ake ciki, Ministan Tattalin Arzikin Iran Ali Madanizadeh ya ce Amurka za ta ci gaba da fuskantar "rashin nasara" nan gaba, yana mai cewa Jamhuriyar Musulunci tana da "shiri na shekaru biyu" don daƙile sabbin takunkumin da Washington ta ƙaƙaba mata.

"Sun yi duk abin da za su iya don fusata ƙudurin al'ummar Iran da jami'an ƙasar, amma sun gaza a kowane lokaci. Da alama suna so su sake shan kashi," kamar yadda Madanizadeh ya bayyan a wata hira da aka yi da shi ta wani gidan talbijin na gwamnati.

"Mun daɗe muna jiran waɗannan tsare-tsaren, kuma a shirye gwamnati take kuma tana da shirin shekaru biyu don gudanar da waɗannan abubuwan," in ji shi.

Iran ta 'yi watsi da' matsin lamba

Babban hafsan sojojin Pakistan ya gana da shugaban majalisar dokokin Iran, Mohammad Bagher Qalibaf a Tehran, yayin da Islamabad ke ƙoƙarin farfaɗo da tattaunawar kai-tsaye tsakanin Iran da Amurka da ta tsaya cak.

Ganawar ta zo ne yayin ziyarar da Munir ke yi a Tehran, inda yake tattauna wa kan sabbin yarjeniyoyin da jami'an Iran bayan zaman baya bayan nan da Washington, kamar yadda majiyoyi da dama na gwamnatin Pakistan suka shaida wa Anadolu.

A cewar gidan talbijin na IRIB na ƙasar Iran, Qalibaf ya shaida wa Munir cewa Washington ta gaza cika alƙawuran da ta ɗauka a ƙarƙashin yarjejeniyar fahimtar juna ta Islamabad. 

"Alƙawuran da ɓangarorin suka ɗauka a ƙarƙashin yarjejeniyar da aka cim ma a bayyane suke, kuma gazawar Amurka wajen kin cika alƙawuran da ta ɗauka, sun hana kwanciyar hankali wanzuwa a yankin, sannan ta samar da wani gaba na shakku kan amincewa da ita," in ji shi.

Qalibaf, wanda shi ma yake jagorantar tawagar tattaunawa ta Iran, ya yi watsi da yiwuwar Tehran ta miƙa wuya ga matsin lambar Amurka, ya kuma ce Iran na bin diddigin aiwatar da sharuɗɗan yarjejeniyar.