A lokacin da Chloe Cole ke 'yar shekaru 13, ta fara fuskantar kalubalen balaga da alamun jinsi biyu. Bayan shekaru biyu, ta nemi shawarar likitoci kuma sun yi mata tiyata aka yanke nonuwanta. Likita daya ne kawai ya gargade ta game da illolin wannan tiyata. Ta yi nadamar kin sauraren shawararsa.
Chloe ta sha fama da cutar sauyawar jinsi, wata cuta da dan adam ke gaza fahimtar shi namiji ne ko mace. Amma kwararru na bayyana cewa yara da suke da wannan cuta suna girma ba tare da fahimtar jinsinsu ba, kuma suna shiga yanayin damuwa da dimauta sakamakon wasu dalilai.
Cole, mai shekaru 18 a yanzu, na daya daga cikin yara mata da suke son komawa mace inda take nadamar yin kuskure na sauya halittarta zuwa namiji.
Cole na son zama uwa wata rana, amma watakila ba za ta taba iya shayar da mama ba.
“Wani abu mai kayatarwa kuma na musamman shi ne yadda gaba daya al'aurata ta rabu da ni har abada. Ina da lafiya sosai kafin yanzu,” ta bayyana haka a yayin wata tattaunawa. “Ina da yarinta sannan”.
Wadannan yara mata, iyayensu da likitocinsu a kasashe da dama na bayyana damuwa game da magani da ke da rikitarwa da ake yi wa yaran kanana.
Batun sauya jinsi ya fito karara ne a lokacin da iyaye da suka damu, suka dinga fafutukar adawa da mayar da kulla alakar luwadi ba komai ba a makarantun firamare.
A Amurka da Ingila da wasu kasashe da ake kira masu karfin tattalin arziki, ana karfafa gwiwar yara da su zabi ‘wakilin sunansu’, wanda a wasu lokutan hakan ke rikitar da kwakwalensu, in ji wani kwararre.
Ta yaya muka kai ga haka?
A shekaru 20 da suka gabata, tunanin ‘kula da lafiyar tabbatar da jinsi’ a tsakanin hukumomin kula da lafiya ya zama abin da ke jawo ce-ce-ku-ce. Batun na bayyana cewa idan yaro ko yarinya ya kidime game da jinsinsu, zai iya neman likitoci su yi masa tiyata domin mayar da shi jinsin da yake son zama.
Matsalar ita ce kananan yara ba su da hangen nesa ballantana su yi hasashen abin da zai je ya komo idan suka yanke wannan hukunci, kuma likitoci ba sa yi musu gargadin da ya dace kafin a yi musu tiyatar sauya jinsi.
“Idan kina 'yar shekara 15 zuwa 16 kuma aka yanke miki nonuwa, a lokacin ba ki kai shekarun fara tunanin ko kina son jariri a nan gaba ba,” in ji Dr. Karleen Gribble, wadda ke aiki a makarantar koyon aikin jiyya da ungozoma a Jami’ar Yammacin Sydney.
“Bayan shekaru 15, kin samu jariri, amma kuma ba ki da nonuwa, kenan ba za ki iya yin komai ba saboda mataki ne da kika yanke na karshe.”
Daga baya, an fara tantance asibitocin da ake tura yara da suke da cutar matsalar rashin sanin jinsinsu.
A watan Fabrairu, tsohuwar ma’aikaciyar Cibiyar Sauyin Jinsi ta Jami’ar Washington da ke Asibitin Yara na St. Louise ta tona asiri a lokacin da ta rubuta wata makala mai cike da suka.
Ta bayyana yadda aka dinga gaggawar sauya wa yara halittarsu ba tare da ba su shawarwarin da suka dace ba.
A wata makala mai taken “The Free Press”, Jamie Reed ta rubuta cewa ana samun yara kanana da ke da cutar kwakwalwa - kamar su hauka bayan fuskantar wata matsala da yawan dimauta, da cutar rashin gane jinsi, kuma hakan ya sanya ake shawartar su da su sauya jinsin nasu.
“Makonni da suka gabata, kusan dukkan matsalolin da Amurka ke fuskanta sun shafi matasa ne.”
Yaduwa a cikin al’umma
A 'yan shekaru kadan baya, mafi yawancin tiyatar da asibitocin ke yi sun shafi yara maza ne. Tun daga 2015, adadin yara mata da ke neman sauya jinsi ya karu sosai.
A Amurka, cutar rashin fahimtar jinsi ta karu sosai zuwa 40,000 a 2021 idan aka kwatanta da shekaru hudu da suka gabata. Wani bincike da Hukumar Lafiya ta Kasa ta Ingila ta gudanar ya gano cewa a 2021 an samu mutum dubu 5,000 da ke son sauya halitta. Kuma kashi biyu cikin ukun su mata ne.
Tunda wannan abu sabo ne, babu wani zuzzurfan bincike da aka yi don gano musabbabin karuwar adadin yara da ke son sauya halittarsu.
Amma bayanan da aka samu daga bakunan mutane yayin tattaunawa da iyaye na cewa kafafen sada zumunta na intanet na taka muhimmiyar rawa a kan hakan. Yara mata balagar fari da ke fama da wannan cuta ta rashin tsayayyen jinsi na kallon tiyatar a matsayin magance rashin farin ciki da kamanninsu.
Yawaitar bayanai da suka shafi sauya jinsi a kafafen sada zumunta na intanet da kuma labarai da ba a tantance su ba a TikTok na taka rawa sosai wajen yanke hukuncin da yara suke yi.
Kwararru na cewa babbar matsalar na tattare da rashin bincike kan makoma ta tsawon lokaci game da sauyin jinsi.
Ta yaya abu yake faruwa
A Ingila da wasu kasashen da ake kira wadanda suka ci-gaba, hanyar sauya jinsi takan fara ne kamar haka: Yarinya za ta fada wa iyayenta cewa tana son sauya sunanta da kamanninta, sai a kai ta wajen likitan mahaukata, wanda bayan wani dan lokaci sai ya tura ta wajen likitan kwayoyin halitta, wanda shi kuma zai dora yarinya a kan magani.
Bicalitamide, wani magani da ake amfani da shi don magance cutar kansa ne ake bai wa yara maza don hana su balaga a siffar maza. Maganin na sauya halittarsu su koma kamar mata.
Maganin ‘Testoterone’ da ake bai wa mata ne ke sanya muryarsu ta zama kakkausa sannan ya sanya su fara fitar da gashi a fuskokinsu.
Idan iyaye suka yi tawaye, sai likitoci su tsorata su da cewar dansu na iya kashe kansa idan ba a bari an yi masa abin da yake so ba.
Gribble, wata mata da take aiki a Jami’ar Western Sydney. ta ce dokokin da ke sanya idanu kan ayyukan sauya jinsi kamar na Kungiyar Kula da Lafiyar Sauya jinsi ta Duniya ba abubuwan dogaro ba ne.
Ta ce “Kamar ba ma sa fadin tiyatar yanke nonuwa sau biyu za ta shafi shayarwa.”
A lokacin da take bincike don makalarta, wadda ta yi hira da wata mace da ta yi nadamar bari a yanke mata nonuwanta, Gribble ta “dimauta” bayan ta gano cewa babu wani alfanu ga yarinyar da ta sha magani ko aka yi wa tiyatar.
“Wasu mujallu na bayar da dama a buga bincike da ya yi babban ikirari da babu wasu hujjoji da za su iya kare shi. Wannan abin damuwa ne kwarai.”
Wata makala ta bincike ta yi bayani kan yadda yara mata suke gamsuwa bayan an cire musu nonuwansu ta hanyar tiyata a asibiti, bayan an tambaye su bayan watanni uku da yin tiyatar.
“Ba za ka iya yin wannan ikirarin ba cikin watanni uku kacal bayan an yi maka tiyata. Watakila bayan shekaru 15, ko 5 ko ma 10, za su iya kwadayin su samu jariri, ta yaya za su yi hakan? Ina tunanin wannan ne abin damuwa. Wannan bincike ba shi da inganci.”