Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta bayyana cewa sinadarin dan-zaki na ‘aspartame’ na iya haddasa cutar kansa.
A wani bincike da Hukumar da ke 'Bincike Kan cututtuka dangin Kansa ta Duniya' karkashin WHO ta gudanar, ta gano cewa akwai alaka tsakanin sinadarin aspartame da wani nau'in cutar kansa ta hanta da ake kira ‘Hepatocellular carcinoma’.
A binciken, wanda ta gabatar a ranar Alhamis, WHO ta ce bayan wasu nazarce- nazarce da ta yi ta gano cewa bai kamata a yi amfani da fiye da 40 mg/k na sinadarin a kullum ba, idan ba haka ba akwai yiwuwar kamuwa da cutar kansa.
WHO ta ce “Aspartame ba shi da illa sosai idan aka sha shi cikin iyakar miligram 40 a kowace kilogiram na nauyin jikin mutum.”
Ana yawan amfani da dan-zaki a cikin abubuwan da ake hadawa na sha da sauran abubuwan da suka hada da Diet Coke da Pepsi Zero Sugar da cingam da ayis kirim da yogurt da ma man goge baki.
Duk dan adam da nauyinsa ya kai kilo 70 ko fam 154 ya sha fiye da gwangwani tara zuwa 14 na lemo ko soda mai dauke da sinadarin aspartame a kullum, to ba shakka ya wuce iyakar da jikinsa ke bukata kuma ya na cikin hadarin kamuwa da rashin lafiya.
Amfani da dan-zaki a madadin sugari
Masana'antu abinci da dama suna amfani da sinadarin aspartame a madadin sukari saboda ya nunka sukari sau 200 wajen zaki, hakan ya sa ake iya amfani da adadi kadan don wadatar da yawan lemon sha da ake so a hada kuma akan samu irin dandanon da ake bukata.
Kimanin kayayyaki 6,000 ne a duniya ke dauke da sinadarin dan-zaki a cikinsu, a cewar hukumar Kula da kuzarin jikin dan adam ta kungiyar ‘yan kasuwa wacce ke wakiltar masana’antun da ke hada kayan zakin da ake amfani da su.
Tun a shekarar 1965 ne wasu masana kimiyya a kamfanin hada magunguna na G.D & co suka gano aspartame, sai daga baya aka fara sayar da shi inda ake kiran sa da sunan NutraSweet . Tun daga lokaci aka amince da sinadarin ya ke ta janyo ce-ce-ku-ce.