A wannan makon masu bincike na kasar Denmark suka cimma matsayar cewa an yi amfani da wasu manyan abubuwan fashewa wajen fasa bututan mai na Nord Stream domin yin zagon kasa, amma kuma ba su dora alhakin hakan kan wata kasa ba.
Swidin da ma ta bayyana cewa sakamakon binc,ken farko da ta yi ya nuna an fasa bututan ne don zagon kasa.
Ana ci gaba da yada jita-jita kan waye zai amfana da lalata bututan na makamashi mai muhimmanci, wanda ya keta ta tekun Baltic. A watan Satumba ne aka fasa bututan man ta hanyar hari.
Masu bincike sojojina yankin sun bayyana da wahala a bayyana wadanda suka yi wannan ta’annati a nan kusa, saboda rikicin da ake yi na Yukren.
Jens Wenzel Kristoffersen, mai bincike a Cibiyar Nazarin Sojoji ta Jami’ar Copenhagen ya bayyana cewa “Ina da tabbacin ‘yan Swidin ba sa son bayyana sakamakon bincikensu a nan kusa. Ba sa son bayyana wani abu kafi su tabbatar da cewa rasha ce ta aikata wannan abu.”
Ya fadawa TRT World cewa “A lokacin da sanarwar ta fito, akwai yiwuwar yanayin tsaro zai tabarbare a tekun Baltic, wanda a baya ake kira Tekun Zaman Lafiya, amma a lokacin da Swidin da Finlan suke kusantar NATO, ana kiran sa da sunan Tekun NATO.”
An lalata uku daga cikin bututan gas na Nord Stream hudu, wadanda aka gina su don daukar albarkatun mai daga Rasha zuwa Jamus da kasashen dake gaba na Turai.
Jami’an kamfanin Blueye Robotic na kasar Noewary da ya kware kan sarrafa jiragen ruwa marasa matuka a karkashin teku, a wannan makon ya fitar da bidiyon wani bangare na bututun da ya lalace, wanda ya bi ta Yankin Tattalin Arziki na Swidin.
Trond Larsen, wanda ya jagoranji aika jiragen marasa matuka zuwa karkashinteku ya bayyana cewa “Wani bangare na bututan ya bace, amma da wahala a fadi yawan abubuwan da suka bace”.
Ya fadawa TRT World cewa, “zan iya fadin a kalla mita 60 na bututun ya lalace kuma ya lankwashe,”.
Akwai alamu karara dake nuna abubuwan da aka yi a tekun, inda ya nuna jamiğ’an Swidin sun je don tattara bayanai.
Ya kara da cewa, Kafin fara yakin a watan Fabrairu, Rasha ce babbar abokiyar Turai wajen samun makamashi, inda take taimakawa wajen samar da kaso 40 na gas din da Turai ke bukata.
A ‘yan watannin nan, an rufe Nord Strem, hakan na janyo karancin makamashi, tashin kudin gas da ake biya wanda hakan ke matsa lamba ga shugabanni a Jamus, Faransa, Italiya da wasu wuraren su fara neman mafita kan yadda za a dumama gidaje.
Me ya sa ba za a yi binciken hadin gwiwa ba?
Denmar, Jamus da Swidin duk sun gudanar da bincike a kashiin kansu kan harin. Da fari dai, an bayar da shawarar kafa kwamitin bincike na hadin gwiwa, amma Swidin ta ki yarda inda ta balle ta fara nata bincike ita kadai.
Ofishin masu gabatar kara na Swidin da ya yi binciken bai bayar da amsa ga tambayar da TRT World ta yi ba, da ta hada da kosun samu wani ko wasu da suke zargi.
Darakta Janar na Hukumar Kula da Tekun Baltic dake Stolkhom, wadda ke wakiltar manufofin kasashen dake gaba da tekun ya ki amsa tambayar me ya sa suka ki samar da kwamitin bincike na hadin gwiwa.
Wani tsohon sojan Swidin Birgediya Janar Carsten Rasmussen mai ritaya ya fadi cewa, watakila dalilin da ya sanya hakan shi ne a ki aiki tare da Rasha, wadda ta nace sai ta zama wani bangare na kwamitin binciken.
Ya kuma fadawa TRT World cewa “Akwai cikakken rashin aminci tsakanin kasashen Yamma uku da Rasha. Suna zargin Moscow ce ta shirya wannan zagon kasan.”
Kamfanin albarkatun gas na Rasha na Gazprom ne ke da mallakin kusan dukkan bututan Nord Stream. Fadar Cremlin ta shaida cewa ba ta da wani dalili da zai sanya ta fasa kayanta, inda ta nuna cewa masu kasuwancin LNG na Amurka ne za su amfana sosai ga tabarbarewar aika gas zuwa Turai.
Rasmussen, wanda ya yi aiki a matsayin jakadan sojin Denmark a Rasha tsawon shekaru uku ya bayyana cewa, al’amarin ya kai matsayin kama da yaki.
Ya ce “Irin wannan hari kan bututtan mai na dasa zargi ga sojoji da ma wadanda ba soji ba. Ba aiki ne na yaki ba. Abun ya faru a wajen iyakokin Denmark da Swidin. Amma dai an gano an yi amfani da kayan fashewa. Saboda haka kana kusa da afkawa yaki ne.
Me ya faru a gaba?
Har zuwa lokacin da mahukuntan Denmark da Swidin za su bayyana sakamakon bincikensu ga jama’a, zai yi wahala a bayyana ta yaya aka aikata wannan zagın kasan a teku, wanda ake kula da shi sosai.
“A shekaru 37 da na yi a rundunar sojin ruwan Denmark ban taba ganin abu irin haka ba”, in ji Kristofferses na jami’ar Copenhagen.
Mahukuntan tekun Mahukuntan sufurin jiragen ruwa na kasashen dake yankin sun gano alamun zuwa jiragen ruwa wajen, ko kuma suna giftawa.
Kristoffersen ya ce, “Amma abun da ya faru a karkashin teku na da wahalar ganowa,”.
Ya ce, Idan aka zo batun tsaro, jami’an kasashen Turai sun zaku tun kafin ma a kai hari kan bututan iskar gas na Nord Stream. A yanzu akwai tattaunawa don nemo hanyoyin da za a bayar da kariya ga wayoyin karkashin teku da bututan.
Kristoffersen ya ci gaba da cewa “A Swidin mun ga karuwar aiyuan jirage marasa matuka a saman cibiyoyin Nukiliya, fankar samar da makamashi daga iska a Denmark. Har yanzu ba a tabbatar da wye ya tayar da jiragen marasa matuka ba. Amma daga ganin girman su an san ba wai na wasa ba ne.”