ChatGPT na daga cikin kirkirariyar basira da ake amfani da su wurin saukaka ayyuka. Hoto/Reuters

Za a sabunta manhajar ChatGPT inda za ta iya tattaunawa da masu amfani da ita ta murya, da kuma amfani da hotuna, abin da zai kara matsar da ita kusa da kirkirarrun basira irin su Siri na kamfanin Apple.

Damar ta amfani da murya “za ta bude kofa ga damarmaki masu yawa na kirkira”, kamar yadda OpenAI ya bayyana a wani sako da ya fitar a ranar Litinin.

Sauran manhajojin kirkirarriyar basira kamar Siri da Google voice assistant da Alexa na Amazon na tafiya ne da na’urorin kamfanoninsu kuma ana yawan amfani da su wurin saka karaurawa a waya ko tunatarwa ko kuma aika sako a intanet.

Tun bayan fitowar manhajar a bara, kamfanoni da dama sun soma amfani da ChatGPT domin yin ayyuka da dama, inda take saukakawa wurin rubutu a kwamfuta da rubuta wakoki da sauransu.

Sabon tsarin na ChatGPT zai kuma ita hada tatsunuyoyi da shirya muhawara.

TRT World