Masallacin Istiklal wanda ke nufin 'yancin kai ne mafi girma girma a Kudu maso-gabashin Asiya wanda ke da girman hekta 9. Hoto: AP

A lokacin da Fafaroma Francis zai fara ziyarar Asiya a mako mai zuwa, ɗaya daga wuraren da zai fara zuwa shi ne babban Masallacin Istiklal da ke Indonesia.

Shugaban mabiya ɗarikar Katolika mai shekara 87 zai gana da wakilan addinai shida da aka amince da su a ƙasar mafi yawan jama'a a Kudu maso-gabashin Asiya da ke fuskantar ƙaruwar rashin aminta da juna tsakanin addinai.

Fafaroma Francis da ya sha fama da rashin lafiya kuma yake tafiya a keken guragu, na da tattaunawa da yawa a yayin ziyarar ta kwanaki huɗu a ƙasar.

Zai fara zuwa Jakarta a ranar 3 da Satumba, inda zai gana da Shugaban Ƙasar Indonesia Joko Widodo.

A Masallacin Istiklal, Malamin ɗan ƙasar Argentina da aka sani da ƙoƙarin kyautata zaman lafiya tsakanin mabiya addinai, zai gana da wakilan Musulmai, Buddha, Hindu, Confusianism, Katolika da Protestan.

Kundin tsarin mulkin Indonesia ya amince da biyun Ƙarshe a matsayin addinai biyu mabambanta.

Kusan kashi 87 na jama'ar Ƙasar su miliyan 280 Musulmai ne, sai dai kuma ita ce ƙasa ta uku mafi yawan Kiristoci a Asiya bayan Philippines da China.

Kashi 2.9 na jama'ar ƙasar ne mabiya ɗarikar Katolika.

Zama da juna lafiya

Masallacin Istiklal wanda ke nufin 'yancin kai ne mafi girma girma a Kudu maso-gabashin Asiya wanda ke da girman hekta 9.

Sunansa na tunatar da yaƙin ƙwatar 'yanci da jama'ar suka yi daga hannun 'yan mulkin-mallaka na ƙasar Holland, da suka shugabance su tsawon shekaru kusan 350.

A daura da Masallacin akwai Majami'ar ta Roman Catholic neo-Gothic Our Lady of The Assumption Cathedral Jakarta.

Kusancin wuraren bautar guda biyu na da ma'ana sosai kan yadda addinai za su iya wanzuwa tare su zauna lafiya, kamar yadda shafin intanet na gwamnati ya bayyana.

Masallacin da majami'ar na haɗuwa da juna ta hanyar ƙarƙashin ƙasa da ake kira "Hanyar Ƙarkashin Ƙasa ta Ƙawance" da ke da tsayin kusan mita 28, kuma an samar da ita don nuna aminta da juna ta fuskanr addini. Ana sa ran Fafaroma zai shiga wannan hanya.

Babban Limamin Masallacin Istiklal Nasaruddin Umar ya faɗa wa The Associated Press cewa zaɓar fara ziyartar Indonesia da Fafaroma ya yi ta sanya 'Musulman Indonesiya farin ciki".

Ya kuma ƙara da cewa za su yi amfani da ziyarar ta Fafaroma don tattaunawa kan kamanceceniyar tsakanin mabiya addinai, ƙabilu da aƙidu daban-daban.

Umar ya kuma shaida cewar al'umma da ke ta daɗuwa da al'ummu mabambanta irin Indonesia na iya fuskantar ƙalubale, "amma muna buƙatar sanin cewa muna gudanar da rayuwa ce bisa ikon Ubangiji".

TRT World