Ana neman siyasantar da yawan kona Al’qur’ani mai tsarki da ke samun gidin zama a tsakanin kungiyoyi masu tsattsauran ra’ayi a Turai / Photo: AA

Mambobin wata kungiyar masu tsattsauran ra'ayi ta kasar Denmark, Patrioterne Gar Live, sun hallara a kofar ofishin jakadancin Turkiyya da ke birnin Copenhagen, dauke da takardun da ke nuna kyamar Musulunci inda suka kona Al-kur’ani da tutar Turkiyya.

Mambobin kungiyar sun kuma yada lamarin wanda ya faru a makon jiya, kai tsaye ta shafin Facebook.

Wannan mummunar aika-aikar ta jawo kakkausar suka tare da Allah-wadai daga Ankara babban birnin Turkiyya, washegarin ranar da abin ya faru.

Ma'aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta ce ba za ta taba amincewa da irin wadannan munanan ayyukan da aka bari suna faruwa ba, da sunan "‘yancin fadin albarkacin baki’’.

"Wannan aika-aikar da aka gudanar a cikin watan Ramadan, ta nuna karara yadda ake kyamar Musulunci da nuna wariya da kuma kyamar baki, lamarin da ya kai wani yanayi mai ban tsoro a Turai, kuma ga dukkan alamu ba a koyi darasi daga abin da ya faru a baya ba," a cewar ma'aikatar.

Ba Turkiyya kadai ba ce ta yi Allah-wadai da matakin wanda ya taba zukatan biliyoyin Musulmai a fadin duniya.

Kasashe irin su Qatar da Saudiyya da kasar Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) da Jordan, da Moroko da kuma Pakistan sun bi sahu wajen suka da yin Allah-wadai da wannan lamari.

"Saudiyya ta yi Allah-wadai da kakkausar murya kan kona Kur'ani mai tsarki da wata kungiya mai tsattsauran ra'ayi a Denmark ta yi a gaban ofishin jakadancin Turkiyya da ke birnin Copenhagen," a cewar wata sanarwa da Ma'aikatar Harkokin Wajen Saudiyyan ta fitar.

Sanarwar ta jaddada cewa "akwai bukatar karfafa dabi'un tattaunawa da hakuri da mutuntawa da kuma watsi da duk wani abu da zai yada kiyayya da nuna tsattsauran ra'ayi da wariya."

Siyasar kiyayya ga Musulmai

Lamarin da ya faru na baya-bayan nan a kasar Denmark, wani salo ne da ke cigaba da yaduwa a nahiyar Turai inda kungiyoyin masu tsattsauran ra'ayi ke amfani da 'yancin fadin albarkacin baki wajen kafa hujja a ayyukan nuna kyama da kiyayya, ta karkashin fakewa da kariyar gwamnati.

A 'yan watannin da suka gabata, Turkiyya na fuskantar karuwar hare-hare daga masu ra'ayin mazan jiya na Turai tun bayan da Ankara ta nuna damuwarta kan yadda kasashe irin su Sweden ke ba da mafaka ga mambobin wasu kungiyoyi da masu goyon bayan ta'addanci.

A watan Janairun da ya gabata wani dan siyasa mai ra'ayin rikau da ke da ruwa biyu dan kasar Denmark da Sweden, ya kona kwafin Kur'ani a kalla sau biyu. ,

Ya yi na farkon a wajen ofishin jakadancin Turkiyya da ke Stockholm, sai na biyun a gaban wani masallaci da ke kasar Denmark, lamarin da ya jawo kakkausar suka daga al’ummar Musulmai a fadin duniya.

Yawan faruwar irin wannan lamari ya tilasta wa Turkiyya fitar da wata sanarwa mai karfi da ke nuna damuwarta game da “haduran da ke tattare da nuna kyama ga addini da kiyayya a kasashen nahiyar Turai.

"Kasashen Turai da ke maraba da irin wadannan munanan ayyukan da ke kona zukatan miliyoyin jama'a na barazana ga yanayin zaman lafiya tare da kara haifar da nuna wariyar launin fata da kyamar baki da kuma kyamar addinin Musulunci a Turai”, in ji sanarwar.

Kazalika Ma’aikatar tsaro ta Turkiyya ta yi Allah wadai da lamarin da ta ce ‘’ abin tsoro ne da tashin hankali da kuma takaici’’ yadda aka mayar da hankali wajen kona Kur’ani mai tsarki da kuma tutar kasar Turkiyya a Denmark.

"Wannan aika-aikar da aka gudanar a cikin watan Ramadan, ta nuna karara yadda ake kyamar Musulunci da nuna wariya da kuma kyamar baki, lamarin da ya kai wani yanayi mai ban tsoro a Turai, kuma ga dukkan alamu ba a koyi darasi daga abin da ya faru a baya ba."

Ma'aikatar Harkokin Wajen Turkiyya

Ma’aikatar ta bukaci mahukuntan Denmark da su gaggauta daukar matakan ladabtarwa kan wadanda suka aikata wannan mummunar aika-aika tare da dakile duk wata hanya da ka iya barazana ga zaman lafiya a tsakanin al’umma.

TRT World